Gwamnatin Kano ta ƙwato motoci daga hannun Kwamishinonin da suka yi murabus




Hukumar ta karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano ta ƙwato motocin gwamnati daga hannun Kwamishinonin da suka yi murabus da kansu daga majalisar zartarwa ta jihar.

Aikin ƙwato motocin, wanda jami’an hukumar suka gudanar a ranar Alhamis, ya biyo bayan zargi kan tsofaffin Kwamishinonin ya nuna wajen ƙin mayar da kadarorin gwamnatin.

Tsoffin Kwamishinonin da lamarin ya shafa sun haɗa da:

  • Air ɓice Marshal Ibrahim Umar (mai ritaya): Tsohon Kwamishinan Tsaron Cikin Gida.
  • Mustapha Rabiu Kwankwaso: Tsohon Kwamishinan Matasa da Wasanni.
  • Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata: Tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha.
  • Dr. Adamu Aliyu Kibiya: Tsohon Kwamishinan Al’amuran Jin ƙai.
  • Hon. Nasiru Sani Garo: Tsohon Kwamishinan Ayyuka na Musamman.

Dalilin ɗaukar matakin

Yayin da yake yi wa manema labarai bayani jim kaɗan bayan kammala aikin, Shugaban Hukumar, Sa’idu Yahaya, wanda shi ne ya jagoranci samamen, ya bayyana cewa ɗaukar matakin ya zama dole bayan da tsoffin Kwamishinonin suka ƙi amsa kiran da aka yi musu na yau da kullum na su mayar da kadarorin gwamnati.

Yahaya ya bayyana cewa, sun gudanar da aikin ne sakamakon ƙorafi da kuma sanarwa da suka samu daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano game da zargin cin zarafin ofis da kuma buƙatar tsofaffin jami’an su miƙa dukkan kadarorin gwamnati da ke hannun su bayan yin murabus.

Zargin sayar da motocin

Shugaban Hukumar ya ƙara da zargin cewa wasu daga cikin Kwamishinonin sun sayar da motocin hukumar jim kaɗan bayan barin ofis.

“Kadarorin gwamnati ba mallakin ƙashin kai ba ne. Da zarar jami’i ya bar ofis, dole ne ya mayar da dukkan motoci da kadarorin gwamnati da ke hannunsa cikin gaggawa,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: “An ba su shawarar su mayar da motocin don kauce wa irin wannan yanayi, amma suka ƙi, wanda hakan ya sa ba mu da wani zaɓi face mu ɗauki mataki. Mun bi ƙa’ida kuma mun sami umarnin kotu wanda aka ba mu damar kwaso motocin.”

Sakamakon Bincike

Hukumar ta bayyana cewa:

  • An kwato motoci biyar daga hannun Kwamishinoni biyar ɗin.
  • Daga cikin biyar ɗin, guda biyu kacal ne ainihin motocin da gwamnati ta saya.
  • Sauran guda ukun ba su ne ainihin motocin da aka ba su ba.

“Bincike ya nuna cewa an sayar da ainihin motocin, sannan aka maye gurbinsu da wasu motocin, waɗanda su ma mun ƙwato su. Za mu ƙaddamar da cikakken bincike don gano ko an sayar da motocin ne don siyan waɗannan ko akasin haka,” in ji Yahaya.

Daga karshe, shugaban hukumar ya karyata zargin cewa matakin na da alaƙa da siyasa, inda ya nanata cewa hukumar tana gudanar da aikinta ne kamar yadda doka ta tanada don kare kadarorin al’umma.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *