Gidauniyar Zakkah da Waƙafi ta ƙaddamar da shirin ciyarwar azumi a Gombe
[ad_1]
Gidauniyar Zakkah da Waƙafi ta Jihar Gombe ta ƙaddamar da shirin tallafin Azumi da Sallah ta hanyar raba abincin buɗa-baki ga marasa lafiya da masu kula da su a Asibitin haihuwa na Zainab Bulkachuwa.
Shirin na daga cikin ayyukan jin ƙai da gidauniyar ke gudanarwa a duk shekara domin rage raɗaɗin matsin tattalin arziki da ke addabar marasa galihu a cikin watan Ramadan mai alfarma.
Shugaban gidauniyar, Dakta Abdullahi Abubakar Lamido, ya ce tallafin na bana ya mayar da hankali ne kan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na al’umma, musamman marasa lafiya da masu jinyarsu da kan fuskanci wahalar samun abincin buɗa-baki yayin da suke azumi.
Ya ƙara da cewa, ana sa ran za a ci gaba da gudanar da shirin ciyarwar har zuwa ƙarshen watan Ramadan, gwargwadon wadatar kuɗin da ake da shi
Dakta Lamido ya yi kira ga masu hannu da shuni da ƙungiyoyi da su mara wa shirin baya domin a samu damar kai tallafin ga ƙarin masu buƙata.
Wasu daga cikin marasa lafiya da masu kula da su sun yaba wa gidauniyar bisa wannan taimako, inda suka bayyana shi a matsayin abin a yaba da ya zo a kan lokaci.
Sun kuma yi kira ga sauran ƙungiyoyi da masu hali da su yi koyi da wannan shiri, musamman a watan Ramadan da ma bayan sa.
Baya ga shirin ciyar da Azumi, gidauniyar na kuma raba kayan sawa, kayan abinci da kuɗaɗe ga marasa galihu da marayu a matsayin wani ɓangare na tallafin a lokacin shirye- shiryen Sallah da ake yi a kowace shekara.

Masu alaƙa
[ad_2]
Source link