Wata Uku Da Kafa Dokar Ta-ɓaci: Har Yanzu Matsalar Tsaro Na Ci Gaba Da Ta’azzara
[ad_1]
Tsawon wata uku kenan yanzu, bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa dokar ta-ɓaci kan tsaro, amma har yanzu kashe-kashe da sace-sacen Ƴan Nijeriya ba su lafa ba.
Hasali ma, da alama an ta’azzara ayyukan ta’addanci, domin kuwa an samu ƙaruwar sace-sacen ƴan Nijeriya ko kuma kashe su a cikin waɗannan Ƴan watanni.
- Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Soke Harajin Da Ta Kakaba Bayan Hukuncin Kotun Kolin Kasar
- Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Dokar Gyaran Zaɓe Duk Da Rikicin Tura Sakamako
A ranar Laraba, 26 ga watan Nuwambar 2025, shugaba Tinubu, ya ayyana dokar ta-ɓaci a dukkanin faɗin wannan ƙasa, tare da bayar da umarnin ƙara ɗaukar sabbin ma’aikata a rundunar soji.
Har ila yau, an ɗauki matakin ne da nufin kawo ƙarshen sace-sacen jama’a da kashe-kashen da ƴan ta’adda da ƴan bindiga ke yi a sassan ƙasar.
Ya ce, “Gwamnatinmu za ta tallafa wa gwamnatocin jihohin da suka kafa jami’an tsaro, don kare jama’arsu daga ƴan ta’addan da ke da niyyar kawo cikas ga zaman lafiyar ƙasarmu.”
Shugaban ya kuma yi kira ga majalisar dokokin ƙasar, da ta fara duba dokokinmu, domin bai wa jihohin da ke buƙatar kafa Ƴan sandan a jihohinsu.
Ya kuma bayar da umarnin a ɗauki manya-manyan ma’aikata na jami’an tsaro a dukkanin faɗin Nijeriya, inda ya umarci Ƴan sanda da su ƙara ɗaukar ma’aikata 20,000, wanda ida aka haɗa za su kai kimanin 50,000 da ake ci gaba da ɗaukar.
Shugaba Tinubu ya kuma bayar da izinin mayar da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), zuwa wuraren horar da ƴansanda na wucin gadi, sannan ya bayar da umarnin a janye jami’an da ke ba da kariya ga mutane na musamman (ɓIP), domin sake horar da su nan take kafin a tura su wuraren da ake fuskantar ƙalubalen tsaro.
Haka zalika, ya bai wa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), damar tura ƙwararrun jami’an tsaron daji, domin fatattakar Ƴan ta’adda da Ƴan bindiga da ke ɓoye a cikin dazuzzukan, ya kuma umarci hukumar da ta ɗauki ƙarin jami’an da za su ƙarfafa aikin. “Ba za a ƙara samun mafakar masu aikata miyagun laifuka ba,” in ji shi.
Shugaban ya kuma yaba wa jami’an tsaron da suka samu nasarar kuɓutar da Ƴan mata 24 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi da kuma masu ibada 38 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kwara, ya kuma ƙara da cewa; ana ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran waɗanda aka yi garkuwa da su, ciki har da ɗaliban da aka sace a Jihar Neja.
Da yake jawabi ga rundunar sojojin, Tinubu ya yaba da jajircewarsu, tare da buƙatar su ci gaba da jajircewa a kamar yadda suka saba.
“Bai kamata a yi sulhu da Ƴan ta’adda ba, babu wani batu na haɗa kai da su, sannan ya kamata ku san cewa; al’ummar Nijeriya da ku suka dogara,” in ji shi.
To sai dai kuma, tun bayan wannan sanarwar, da alamun kashe-kashe da sace-sacen jama’a na ƙara ta’azzara, koda-yake, hukumomin tsaro sun dage cewa; suna kan gaba wajen shawo kan al’amarin taɓarɓarewar tsaron.
Alal misali, hedikwatar tsaro ta ce; ta fara jigilar dakaru na musamman da kayan aiki zuwa yankuna masu nisa.
Rundunar sojin Nijeriya ta kuma yi iƙirarin cewa; ta tura ƙarin dakaru na musamman Jihohin Benuwe, Plateau, Nasarawa da Taraba, domin ƙarfafa ayyukan yaƙi da ta’addanci.
A cewar hukumomin sojin, waɗannan matakan sun kai ga kawar da Ƴan ta’adda da dama da suka haɗa da wasu shugabanninsu.
A baya-bayan nan, daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya bayyana cewa; an kashe shugabanin Ƴan ta’adda da dama, yayin da wasu suka miƙa wuya ga sojoji a sansanoni daban-daban.
Ya ƙara da cewa, a cikin watan Janairu kaɗai, sojoji sun kashe Ƴan ta’adda da dama, tare da kame mutum sama da 270 da ake zargi da kuma kuɓutar da mutum 230 da aka yi garkuwa da su a wani samame a yankin Arewa.

Daga cikin waɗanda aka kawar, a cewar hedikwatar tsaron, akwai Munzir, wanda aka fi sani da Baa Yanziye, tare da wasu a yayin hare-haren ta sama. Bugu da ƙari, an kama ƴan ta’adda kimanin 34 a cikin makwanni biyu a yankin Arewa maso Gabas.
Har ila yau, an ce; wani shugaban Ƴan ta’adda mai suna Yakubu Adamu, ya miƙa wuya ga sojoji da makamai da alburusai a yankin Azir Wajiroko.
Sojojin sun ƙara damƙe mutum 34 da ake zargi, tare da ceto mutum 17 da aka yi garkuwa da su, da dai sauran nasarorin da aka samu a aikin farmakin.
[ad_2]
Source link