‘Babu abin da zai hana Musulmi yi wa tsarin Shari’a biyayya’
[ad_1]
Majalisar ƙoli kan harkokin shari’ar Musulunci a Najeriya (SCSN) ta yi gargaɗin gudanar da Shari’a a Najeriya da ma duniya baki ɗaya, tsari ne na Ubangiji wanda Musulmi ke amfani da shi wajen tafiyar da al’amuransu na kashin kai da na al’umma, kuma babu wani iko ko hukuma da za ta iya sa Musulmi su yi watsi da yin amfani da ita.
Sakatare Janar na majalisar, (SCSN) Nafiu Baba Ahmad, a cikin wata sanarwa da ya fitar a matsayin martani ga rahoton baya-bayan nan da aka gabatar wa Majalisar Dokokin Amurka, ya ce shawarwarin da aka bayar sakamakon tunani ne irin na Turawan Yamma (Epsteinian Western mentality).
Idan za a iya tunawa, wakilin Amurka na gunduma ta 2 ta West Virginia, Riley Moore, da Chris Smith, Shugaban Kwamitin Harkokin Waje na Afirka na Majalisar, sun gabatar da wani rahoto ga Majalisar Dokokin Amurka bayan wani bincike da suka gudanar kan takurawa Kiristoci a ƙasar nan.
Rahoton ya nuna cewa Shari’a da dokokin savon Allah (blasphemy) su ne manyan matsaloli.
Saboda haka, shawarwarin sun haɗa da soke dokokin Shari’a da na savon Allah, qulla yarjejeniyar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya, da kuma sanya takunkumi ko hana biza ga waɗanda suka aikata hakan.
’Yan majalisar dokokin Amurka sun ce: “Dokokin savon Allah a jihohin Arewacin Najeriya ana amfani da su ne wajen murƙushe ’yancin magana da ra’ayi, yunqurin cin zarafin Kiristoci da tsiraru, da kuma ba da hujjar abin da suka kira ‘hukunce-hukunce’ ba tare da bin tsarin shari’a mai adalci ba.”
To sai dai majalisar ta ce rahoton ya fassara Najeriya a matsayin abin da suka kira da “kisan kiyashi ga Kiristoci”, kuma ya nuna rashin adalci wajen tantama kan haƙƙin Musulmin Najeriya na yin amfani da Shari’a wanda ba za a iya tauyewa ba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link