Likitoci sun yi tiyatar dashen mazakuta a Yobe
[ad_1]
A wani abin ban al’ajabi, likitoci sun yi nasarar sake dasa mazakutar wani mutum da ya yanke nasa da wuƙa a garin Bama da ke Jihar Borno.
Mutumin mai suna Modu Isa, ɗan shekara 50 daga unguwar Hausari, ya girgiza al’umma a ranar Juma’ar da ta gabata bayan da ya daɓa wa kansa wuƙa sau uku, sannan ya yanke gabansa.
Ya bayyana cewa ba ya ganin amfanin gabansa tun da matar da suka rabu, Bayanɗe Modu, ta ƙi dawowa sakamakon zargin da ake yi mata saki uku.
“Ya ce idan Bayanɗe ba za ta dawo ba, to gabansa babu amfani,” in ji wani maƙwabcin Modu, wanda ya tabbatar da cewa matar har yanzu ta ƙi amincewa da batun komawa.
Majiyoyi a Babban Asibitin Bana sun tabbatar da cewa an yi nasarar dawo da gaban nasa, kuma a halin yanzu yana raye yana karɓar magani.
Mazauna garin Bama suna ta tattauna wannan lamari, suna bayyana cewa Modu ya kafa tarihi a matsayin mutum na farko da ya aikata irin wannan abu, wanda za a ci gaba da tunawa da shi.
A halin da ake ciki, majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an mayar da lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) da ke Maiduguri, domin yin hakan laifi ne da ya shafi ɓangaren binciken manyan laifuka.
Al’umma dai har yanzu a rabe suke: wasu na nuna juyayi da baƙin ciki kan faruwar lamarin, yayin da wasu ke mamakin abin da ya faru.
“Maimakon ya yanka albasa don yin miya, sai kuma ga shi ya yanka gabansa,” in ji wani mazaunin garin cikin murmushi da girgiza kai.
Wani dattijo daga unguwar Hausari, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce: “Wannan ba yunƙurin kashe kansa ba ne, wannan barkwanci ne a Borno. A Borno ne kawai mutum zai iya rasa gabansa a ranar Juma’a, kuma a dawo da shi ranar Lahadi.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link