Harin Filato: JNI Ta Tabbatar Da Kashe Mambobinta 4, 10 Sun Ɓace
[ad_1]
Reshen Jama’atu Nasril Islam (JNI) na jihar Filato ya tabbatar da cewa an kashe musulmai hudu yayin da wasu goma suka bace sakamakon harin da aka kai a daren Lahadi a Anguwan Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
Aƙalla mutane 27 ne suka rasa rayukansu a lamarin. Rahotanni sun bayyana cewa maharan, waɗanda ake zargin sun sanya kayan soji ne akan babura, sun kai farmaki Anguwan Rukuba da misalin ƙarfe 7:30 na yamma a ranar Lahadi, inda suka buɗe wuta kan mazauna yankin, lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici.
- Amincewa Da Lamunin Dala Biliyan 6 cikin Sa’o’i 4: Atiku ya caccaki Tinubu da Majalisar Dattawa
- Jirgi Marar Matuki Na Dakon Kaya Samfurin Changying-8 Ya Yi Nasarar Tashi A Karon Farko
Da fari, harin ya yi sanadin mutuwar mutane 14. Daga baya, wasu fusatattun matasa yayin gudanar zanga-zanga, sai suka fara tare masu babura da fasinjojinsu. Majiyoyi sun ce daga bisani wasu mutane 13 da suka samu raunuka, sun rasu a asibiti, wanda hakan ya ƙara yawan waɗanda suka rasu zuwa 27.
A cikin wata sanarwa da sakatarenta, Dakta Salim Musa Umar, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana cewa rahotanni daga al’ummomin Musulmi sun nuna cewa Musulmai ma na cikin waɗanda lamarin ya shafa.
[ad_2]
Source link