Bayan Shekara 20 Nijeriya Ta Sake Dawo Da Tsarin Bayar Da Hayar Kananan Jiragen Sama
[ad_1]
Ministan Surin Jiragen Sama da Kula da Sararin Samaniya Festus Keyamo, ya bayyana cewa, a ranar 6 ga watan ukutobar 2025, Njeriya za sake dawo wa cikin yarjejeniyar bayar da hayar kananan Jirgin Sama.
Wannna na zuwa ne, bayan shekaru 20 da suka gabata, da dakatar da kasar daga cikin yarjejeniyar.
Ministan ya sanar da cewa, an sake dawo da Nijeriya cikin yarjejeniyar ce, biyon bayan kyawawan sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ta samar a fannin na Sufurin Jiragen Sama na kasar wanda hakan ya sanya, ake samun saukin kasashe kudade.
Keyamo ya bayyana haka a taron kaddamar da samar da samar da sararin saukar Jiragen Sama wato na aikin yin garanbauwl wanda ya aka gudanar a filin tashi da saukar Jiragen Sama na kasa da kasa na Murtala Muhammed da ke a jihar Legas.
Ministan ya kara da cewa, ya sanar da cewa, ya kuma mika wata wasika domin ganin an kaddamar da wannan yarjeniyar.
Ita dai wannan yarjeniyar wadda wanda mamallakin karamin Jirgin Sama, zai bayar da hayar Jirginsa na Sama, ba tare da ma’aikata da kula da Jirgin da kuma yin inshore ba.
Akasarin wannan yarjeniyar ana yinta da takardar shedar mamallakan Jiragen Samn wato AOC.
“Hakan ya nuna cewa, mun fara shiga cikin matakin fafada harkar kasuwanci mai zaman kansa ne kuma za mu yi hakan a bangaren Kamafnin Jirgin Sama na Air Peace ba ne, sai dai kawai, a bangaren sauran Jiragen Sama,” A cewar Manajin Darakantan.
A shekarar 2024 ne dai, aka cire Nijeriya daga cikin jeren kasasshen da suka yi kaurin suna wajen saba yarjeniyar, ta bayar da hayar Jirgin Sama.
Kazalika, hakan ya biyo bayan kiyaye daukacin ka’idojin cimma yarjejeniyar da aka kaulla ta Cape Town
Hakazalik,a a shekarar ta 2024 kara sanya Nijeriya a cikin jeren kasashen da aka dakatar a cikin yarjeniyar ta kai daga kaso 70.5 zuwa kaso to 75.5.
Sai dai, bisa sakamakon AWG da babban Jirgin Sama na Boeing da na kananan kamfanonin Jiragen Sama ke jagoranta ne, suka suka cire Nijeriya, daga cikin jeren kasashen da aka dakatar daga cikin yarjejeniyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp
[ad_2]
Source link