Nijeriya Da Saudiyya Sun Ƙara Ƙarfafa Alaƙa Kan Inganta Harkokin Hajji Da Umrah

[ad_1]

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da Masarautar Saudiyya sun sake jaddada aniyarsu ta ƙarfafa haɗin guiwa a harkokin gudanar da Hajji da Umrah, biyo bayan wani muhimmin taro da manyan jami’an ƙasashen biyu suka gudanar an Abuja.

Mai taimakawa Shugaban NAHCON a bangaren yada labarai, Ahmad Mu’azu, ya ce taron ya haɗa hukumomin Nijeriya da wata tawaga daga Saudiyya ƙarƙashin jagorancin Ministan Hajji da Umrah na Masarautar Saudiyya, Dakta Tawfiq Al-Rabiah. An bayyana ziyarar a matsayin wata muhimmiyar alama ta ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman wajen kula da alhazan Nijeriya.

  • Gwamnatin Kano Ta Amince Da Ɗaukar Likitoci ‘Yan Asalin Jihar Aiki Kai-tsaye
  • Kotu Ta Yanke Wa Ɗan Fashi Hukuncin Kisa A Nasarawa

Da yake maraba da tawagar, Shugaban Hukumar Kula da Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman, ya ce ziyarar ta nuna ci gaba da haɗin guiwar Saudiyya da Nijeriya wajen yi wa Baƙin Allah hidima. Ya yaba wa Masarautar bisa ƙoƙarinta na inganta jin daɗin alhazai da samar da ababen more rayuwa da tabbatar da tsaro da kuma inganta ayyukan Hajji da Umrah, musamman ta hanyar shirin Saudi ‘Vision 2030’.

Farfesa Abdullahi Usman ya gamsu cewa akwai wasu ƙalubale da suka shafi bizar Umrah ga ’yan Nijeriya, musamman matsalar tsawaita zama bayan wa’adin izini daga wasu alhazai. Ya jaddada cewa Nijeriya za ta yi aiki kafada da kafada da hukumomin Saudiyya domin shawo kan matsalar, ta hanyar tsaurara sa ido kan kamfanonin da ke da lasisi da inganta tsarin bayanai da kuma wayar da kan allumma.

Ya kuma tabbatar da cewa NAHCON za ta bi duk ƙa’idoji da umarnin Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, tare da kare mutuncin harkokin Hajji da Umrah da muradun alhazan Nijeriya.

A jawabinsa, Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana ziyarar a matsayin tarihi, yana mai cewa wannan ne karo na farko da Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya ya ziyarci Nijeriya. Ya isar da gaisuwa da fatan alheri daga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ga Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud da kuma Yarima mai jiran gado, Muhammad bin Salman.

Ministan ya ce Shugaba Tinubu yana matuƙar girmama Saudiyya, tare da ƙudirin ƙarfafa tsohuwar dangantaka mai ɗorewa tsakanin ƙasashen biyu. Ya ƙara da cewa haɗin guiwa a harkokin Hajji da Umrah na daga cikin muhimman ginshiƙan alaƙar Nijeriya da Saudiyya, wadda ta samo asali daga addini da dadaddiyar alaƙar al’umman biyu.

A nasa ɓangaren, Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dakta Tawfiq Al-Rabiah, ya bayyana cewa Masarautar na da cikakken shiri na ci gaba da aiki tare da Nijeriya domin tabbatar da sauƙi da tsaro ga alhazan Nijeriya. Ya ce a shekarar 2025, sama da ’yan Nijeriya 89,000 ne suka gudanar da Umrah, inda kashi 92 cikin 100 suka shiga Saudiyya da bizar Umrah.

Ya ƙara da cewa an samar da kusan jirage 420 daga Jeddah domin tallafa wa harkokin Umrah ga ’yan Nijeriya, yana mai nuna fatan ci gaba da haɗin guiwa wajen shirin Hajjin 1447 Hijira (2026), domin inganta tsaro da ayyuka da sauƙaƙe harkokin Hajji da Umrah.

A ƙashen taron, ɓangarorin biyu sun amince da ci gaba da haɗin kai da ɗaukar matakai masu amfani domin inganta harkokin Hajji da Umrah, tare da tabbatar da jin daɗi da kare mutuncin alhazan Nijeriya, Baƙin Allah da al’ummar Musulmi baki ɗaya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *