Shugaban Jam’iyyar APC Ya Gana Da Gwamnan Bauchi Kan Batun Sauya Sheƙarsa

[ad_1]

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya gana da gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a ranar Laraba a Bauchi.

Ya gana da shi tare da gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

  • Sanatan Kwara Ta Arewa Umar Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Gwamna
  • Jakadan Sin a Najeriya Ya Halarci Bikin Kaddamar Da Aikin Cibiyar Samar Da Wutar Lantarki Ta Karfin Ruwa A Najeriya

An yi ganawar ne cikin sirri, kuma babu wanda ya yi magana da manema labarai bayan kammala taron.

Majiyoyi sun ce ziyarar na iya kasancewa wani ɓangare na shawo kan gwamnan kada ya koma ADC, face jam’iyyar APC.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan Gwamna Bala ya gana da shugabannin ADC ƙarƙashin jagorancin Babachir Lawal.

A baya, Bala ya ce yana tunanin barin PDP ne saboda rikice-rikicen cikin gida.

Ya ƙara da cewa har yanzu yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki, amma a yanzu ADC ce ta fi dacewa da shi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *