Amurka Ta Tura Sojojinta Zuwa Nijeriya Don Taimakawa Yaƙi Da ’Yan Ta’adda

[ad_1]

Gwamnatin Amurka ta tabbatar da tura wata tawagar sojoji zuwa Nijeriya domin taimakawa wajen yaƙar ’yan ta’adda.

Wannan na zuwa ne makwanni bayan Amurka ta kai hare-hare ta sama kan wasu sansanonin ’yan ta’adda.

  • Gwamnatin Kano Ta Amince Da Ɗaukar Likitoci ‘Yan Asalin Jihar Aiki Kai-tsaye
  • EFCC Ta Kama Jarumar Kannywood, Samha Inuwa, Bisa Zargin Wulaƙanta Takardun Naira

Rahotanni sun ce shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayar da umarnin kai hare-hare ta sama tun watan a Disamban da ya gabata, inda ya ce za a ci gaba da ɗaukar matakan soji kan duk wata barazana ga rayukan jama’a.

Sojojin Amurka sun shafe watanni suna aikin leƙen asiri daga Ghana kafin a turo wasu zuwa Nijeriya.

Kwamandan rundunar sojin Amurka da ke kula da Afirka ya ce an tura sojojin ne bayan amincewar gwamnatocin ƙasashen biyu, sai dai bai bayyana adadinsu ba.

Ministan tsaron Nijeriya ya tabbatar da haɗin gwiwa da sojojin Amurka, inda ya ce suna taimakawa wajen tattara bayanai da kuma kai hare-hare kan sansanonin ’yan ta’adda.

Gwamnatin Tarayya ta kuma ce tana yaƙar dukkanin ƙungiyoyin da ke kashe Musulmi da Kirista ba tare da bambanci ba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *