Ko babu Kwankwaso Abba zai ci zabe

[ad_1]



Gwamnatin Kano ya karyata ikirarin da ke cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ba zai iya samun wa’adin mulki na biyu ba sai da goyon bayan tsohon gwamna kuma jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana haka a martaninsa ga furucin Injiniya Buba Galadima, wanda ya ce siyasar Gwamna Abba ba za ta dore ba, bayan zaben 2027, saboda ya raba gari da Kwankwaso.

Ya bayyana wannan ikirari na Buba Galadima a matsayin kuskuren fahimtar tarihin siyasar Kano da al’adun dimokuradiyya, yana mai jaddada cewa nasarar zabe a jihar ta dogara ne da aiki da karɓuwa a wurin jama’a, ba ubangida ba.

“Tabbas Sanata Rabiu Musa Kwankwaso babban ɗan siyasa ne mai tasiri. Amma cewa makomar siyasar Kano ta a hannun mutum ɗaya take kuskuren tarihi ne,” in ji Waiya a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi.

Ya tuna da yadda tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau ya lashe zabe a 2003 ba tare da goyon bayan wani uban gidan siyasa ba, haka kuma Kwankwaso ya dawo mulki a 2011 bisa tarihin ayyuansa, ba wai an nada shi ba.

Waiya ya kara da cewa Gwamna Abba bai hau mulki ta hanyar alheri na siyasa ba, illa dai ta hanyar kuri’un jama’a da aka kare ta tsarin kundin mulki.

Ya ce gwamnan ya fara kafa tubalin jagoranci ta hanyar sauye-sauyen gwamnati musamman a fannin ilimi, sake gina cibiyoyi da kuma daidaita al’umma. “Mulki a Kano ana tabbatar da shi ne ta hanyar aiki da lokaci, ba ta hanyar gado ko kusanci da wani ba,” inji shi.

Kwamishinan ya kuma kare matakin gwamnan na barin NNPP, yana danganta shi da rikice-rikicen cikin gida, sabanin shugabanci da kuma shari’o’in da ba a warware ba a jam’iyyar.

Ya ce wadannan matsaloli sun raunana tsari da karfin jam’iyyar, tare da haifar da rashin tabbas a matakin jiha da kasa. “An dauki wannan mataki ne da niyyar alheri ga Kano, ba tare da wata mugunta ba, tare da ci gaba da jajircewa wajen zaman lafiya, hadin kai da cigaba,” inji Waiya.

Ya bayyana kwarin gwiwa cewa ba baya ya samun wa’adi na biyu, Gwamna Abba zai kuma yi mulki cikin kwarewa idan aka sake zabensa, domin jagoranci yana kara ƙarfi da gogewa.

A karshe, Waiya ya bukaci ’yan siyasa su mutunta tsarin dimokuradiyyar Kano, yana mai cewa jihar ta Kano kullum tana ba da lada ga aiki, ba ga kusanci da wani jagora ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *