Tun Ina Yarinya Sana’ar Fim Ke Burge Ni —Hafsat Salisu
[ad_1]
Shafi ne da yake zakulo muku fitattun jarumai manya da kanana masu tasowa, daga cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood. A yau ma shafin na tafe da wata jarumar wacce ta shafe tsahon shekaru a cikin masana’antar Kannywood wato, HAFSAT SALISU wacce aka fi sani da HAJIYA HAFSAT inda ta bayyana wa masu karatu batutuwan da suka shafi rayuwarta da kuma sana’arta ta fim.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar Jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki tare da sunan da aka fi saninki da shi.
Ni sunana Hafsa Salisu, amma an fi sanina da Hajiya Hafsa.
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Ni dai a takaice an haife ni a Guru, amma mahaifina Bakano ne ni, ma ina daune a garin Kano ‘Yar Gaya Dawakin Kudu. An yi min aure lokacin ina da shekara goma sha bakwai 17, ina da yara bakwai, yanzu kuma shekara ta 48, wannan shi ne a takaice.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Ni dai tun ina yarinya sana’ar fim take burge ni, saboda yadda suke fadakar da mutane.
Za ki yi kamar shekara nawa da fara fim?
Zan yi kamar shekara goma da fara fim.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Eh gaskiya na sha gwagwarmaya kafin na a fara kirana aiki, sai da nai shekara biyy na nan- na je can, sannan na samu aka fara kira na. Wataran ma sai an kira ni aikin na je na wuni ba a yi da ni ba, sai dai nayi kudin mota na dawo.
Ya batun iyaye lokacin da za ki sanar musu kina son ki fara harkar fim, ko akwai wani kalubale da ki ka fuskanta daga wajensu?
Gaskiya ni ban samu kalubale a gun mahaifiyata ba, dana fada mata ta amince.
Da wane fim ki ka fara?
Na fara da fim din ‘Ahali’.
Ya farkon farawar ta kasance?
Ba komai sai alkairi, saboda dama ka riga ka yi tirenin, dan haka ina yi suka yaba.
Da su wa ki ka fara haduwa a farkon shigarki kannywood?
Hauwa farar lema, Zulai Bebeji, Adaman Kamaye.
Daga lokacin da ki ka fara kawo iyanzu, kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?
Gaskiya babu adadi suna da yawa, ba zan iya lissafawa ba.
Ko za ki iya fadowa masu karatu sunayen kadan daga cikin finafinanki?
Akwai; Kishiyata, Dadin Kowa, Baby, Suwaiba, da dai sauransu.
Cikin finafinan da ki ka fito wanne ne ya zamo bakandamiyyarki, wanda ki ka fi so, kuma me ya sa?
Suwaiba, saboda a garinmu aka zo aka yi, sannan na fito a wurare da yawa.
Wane irin nasarori ki ka samu game da film?
Gaskiya na samu nasara da dama, kuma yanzu ma muna kan samu. Saboda duk inda na je ana girmama ni, kuma ana daukata da muhinmanci. shi ma wannan, babbar nasara ce.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta bayan shigarki cikin masana’antar?
Gaskiya ni babu wani kalubale dana taba samu.
Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farinciki ko akasin haka, wanda ba za ki taba iya mantawa da shi a rayuwa ba?
Gaskiya ni dai kodayaushe a cikin farinciki nake, ni dai ban taba fuskantar wani bakin cikii ba.
Ko kina da ubangida a masana’anyar Kannywood?
Eh iyayen gidana suna da yawa, Baba gumel Nura.
Kafin shigar ki masana’antar Kannywood wadanne jarumai ne suke burge ki, kuma me ya sa?
Ali Nuhu da Adam A. Zango, Gardali Miko, saboda suna fadakar da mu.
Mene ne burinki na gaba game da fim?
Ni dai buri na shi ne, na zama kowa ya san fuskata, na shahara, na yi suna.
Bayan fim kina wata sana’ar ne?
Eh, ina sana’o’i da yawa ma, ina sayar da kayan abinci kamar shinkafa, Dawa, Masara, har itace ina siyar wa da Doya, da Dankalin Turawa, dana Hausa.
Shin za ki iya auren dan fim?
Eh, zan iya aurensa.
Wasu na kokawa game da masana’antar kannywood, a takaice ya za ki yi wa masu karatu bayani game da masana’antar, shin wace ce Kannywood ya cikinta yake?
Ita dai Kannywood masana’anta ce tsarkakakkiya, akwai hadin kai da mutunta juna.
Wane kira za ki yi ga masu kokarin shiga kannywood?
Ina yi musu fatan alkairi yadda muka shiga da kafar dama, su ma Allah ya basu sa’ar shiga lafiya.
Ko akwai wata shawara ko wani sako da ki ke da shi ga sauran abokan aikinki?
Ni dai shawarar da zan bayar a nan duk inda aka kira mu aiki mu zauna lafiya mu tsare mutuncin kanmu.
Me za ki ce da masoyanki masu kallon finafinanki?
Ina yi musu fatan alkhairi, ni ma ina son su.
[ad_2]
Source link