Mutum 612 sun rasa matsuguni sanadiyyar ambaliya a Potiskum — NEMA
[ad_1]
Mutum sama da 600 sun rasa matsuguni sanadiyyar wata mummunar ambaliya da ta afku a garin Potiskum da ke Jihar Yobe.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta bayyana cewa kimanin mutane 612 ne ta samarwa matsuguni bayan ambaliyar ruwa ta mamaye sama da gidaje 102 a garin Potiskum.
Wannan ambaliya ta afku ne a ranar Juma’a 15 ga watan Agusta shekara 2025.
NEMA tare da haɗin guiwar ma’aikatar ba da agaji ta jihar SEMA, sun killace mutanen a wani sansanin wucin gadi da aka kafa a makarantar firamare ta Sabon Gari, yayin da wasu ke samun mafaka a wurin ‘yan uwa da abokan arziki.
Ya zuwa yanzu, jami’an hukumomin NEMA da SEMA tare da haɗin guiwar Ƙungiyar Red Cross, IOM, ICRC da Cibiyar Kare Fararen Hula daga Rikici na ci gaba da aikin ceto da rarraba agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link