NNPP ta lashe zaɓen Bagwai/Shanono a Kano
[ad_1]
Jam’iyyar NNPP wato New Nigeria Peoples Party, ta lashe zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin tarayya da aka gudanar a ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono da ke Jihar Kano.
Babban jami’in da ya tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Hassan Adamu ne ya bayyana hakan da misalin ƙarfe 12:36 na daren Asabar wayewar gari Lahadi.
Farfesa Hassan Adamu Shitu, ya bayyana ɗan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 16,198, inda ya kayar da ɗan takarar jam’iyyar APC —All Progressives Congress — wanda ya samu ƙuri’u 5,347.
Dokta Ali Hassan Kiyawa na jam’iyyar NNPP shi ne ya yi nasara a kan Ahmad Muhammad Kadamu na jam’iyyar APC bayan zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link