Kwastam Ta Miƙa Miyagun Ƙwayoyi Na Miliyan 99.9 A Sakkwato

[ad_1]

Hukumar Kwastam ta Ƙasa a yankin Sakkwato da Zamfara ta kama miyagun ƙwayoyi na naira miliyan 99.9 a hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA a Sakkwato.

Kuntorolan yankin na Kwastam, Aliyu Musa- Ndako ne ya hannun ta haramtattun kwayoyin a hannun kwamandan rundunar NDLEA a Sakkwato.

  • Tinubu Ya Buƙaci Gwamnoni Su Tallafa Wa Talakawa Tare Da Inganta Haɗin Kai
  • Tsarin 60/40: Ana Shirin Tankaɗe Da Rairaya A Majalisar Zartarwar Kano

Ndako ya ce rundunar sintirin jami’an Kwastam ta cafke kayayyakin da aka kwace bayan da wani da ba a san ko wane ne ba ya yi watsi da su a kauyen Maidoro da ke kan titin Sakkwato zuwa Illela.

Ya ce miyagun kwayoyin sun hada da kwali 182 na maganin tari na CST mai dauke da sinadarin kodin da kuma kwayoyin NASACAM Piroxicam wadanda ake zargin an shigo da su ne a cikin kasa ta haramtacciyar hanya.

Ya bayyana cewar hannun ta kayan na cikin umurnin shugaban hukumar Kwastam na kasa, Bashir Adewale na a mika haramtattun kwayoyin a hannun hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *