Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a Kogi
[ad_1]
’Yan bindiga sun kai hari shingen bincike na ’yan sanda a Jihar Kogi, inda suka kashe jami’ai da wani mutum.
Harin farko ya faru da misalin ƙarfe 10:30 na safe a ƙauyen Abugi da ke Ƙaramar Hukumar Lokoja.
Maharan, sun kai harin ne a kan babur, inda suka buɗe wa ’yan sandan da ke bakin aiki wuce.
Wani matashi da ya zo wucewa ta wajen ya rasa ransa.
Bayan haka, maharan sun kwashe bindigogin jami’an sannan suka tsere.
Daga baya, da misalin ƙarfe 11 na safe, suka sake kai wani hari a shingen da ke kan hanyar Ilafin, Isanlu a Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas, inda suka kashe wasu ’yan sanda biyu na rundunar MOPOL 70.
Mutanen yankin sun ce wannan hari ya jefa su cikin tsoro, suna ganin cewa maharan na neman bindigogi ne domin su ci gaba da kai hare-hare.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas, Dokta Joshua Dare, ya yi Allah-wadai da hare-haren.
Ya bayyana harin a matsayin barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.
Ba wannan ne karo na farko da irin wannan hari ya auku ba.
A ranar 9 ga watan Satumba, an kashe jami’an tsaro guda biyar; ciki har da ’yan sanda uku da ’yan banga biyu, a wani hari kwanton ɓauna da aka kai musu a yankin Egbe da ke Ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma.
Gwamnatin Jihar Kogi, a baya-bayan nan ta zargi wasu matasa da taimaka wa ’yan bindiga a yankin, inda ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauke su a matsayin ’yan ta’adda.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP William Aya, bai ce komai game da sabon harin ba, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link