Babban Yankin Guangdong-Hong Kong-Macao Ya Zage Damtse Don Gina Babban Muhallin Kirkire-kirkiren Kimiyya Da Fasaha Na Duniya

[ad_1]

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, “Ya kamata babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao ya mai da hankali kan tsara dabarun gina cibiyar kirkire-kirkire ta kimiyya da fasaha ta duniya, da kokarin gina wani babban muhalli na kimiyya da fasaha na duniya, da karfafa ci gaban sabbin masana’antu masu tasowa.”

To, yaya saurin habakar hadin gwiwa zai iya kasancewa a babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao a yau? Yanzu, a bisa matsakaicin yanayi, duk cikin sa’o’i biyu, ana amfani da izinin hakkin mallaka na kirkira na manyan matakai a aikace a babban yankin kuma cikin sauri ake sada lamarin da tsarin masana’antu tun daga matakin samar da kayayyakin da za a sarrafa zuwa fitarwa. A cikin sa’o’i 48 kacal, ana isar da na’urorin yin gwaje-gwaje tsakanin Guangdong, Hong Kong da Macao zuwa dakin gwaje-gwaje don “dubawa cikin gaggawa da zarar an gabatar da bukatar hakan”.

Yawan ayyukan bincike na hadin gwiwa tsakanin Guangdong, Hong Kong da Macao ya karu da kashi 40 cikin dari. Yanzu, a babban yankin, a bisa matsakaicin yanayi, ana bayar da izinin hakkin mallakar kirkira fiye da 400 a kowace rana. Babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao, wanda ke da kasa da kashi 0.6 cikin dari na fadin kasar Sin, yana samar da kashi 1 bisa 9 na adadin abubuwan da ake samarwa na tattalin arzikin kasar, kuma ya zama daya daga cikin yankunan da ke bude kofa mafi girma ga kasashen waje da kuma karfin tattalin arziki a kasar Sin.

A halin yanzu, bisa mayar da hankali kan sabbin harkoki kamar tattalin arzikin ababen hawa masu tashi kusa da doron kasa da masana’antun sarrafa halittu, babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao zai samar da wasu rukunan sabbin masana’antu guda biyar da kowanensu ya kai fiye da yuan biliyan 100, tare da karfafa saurin ci gaba mai inganci da sauye-sauye na fasaha da inganta masana’antu masu alfanu kamar na gudanar da harkokin sadarwa da kera manyan kayan aikin masana’antu na zamani. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *