’Yan bindiga sun sanya wa mazauna ƙauyen Kebbi harajin N100m ko su ɗanɗana kuɗarsu

[ad_1]



A yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, wasu ’yan bindiga sun nemi malamai mazauna wani ƙauye a Jihar Kebbi da su biya harajin naira miliyan 100 ko kuma su ɗanɗana kuɗarsu.

Wannan lamari dai ya tayar da hankula a garin Utouno da ke Ƙaramar Hukumar Ngaski, inda rahotanni ke nuna cewa ’yan bindigar sun haramtawa duk wani wa’azi ko karatun addini a watan azumin Ramadana matuƙar ba a biya kuɗin da suka nema ba.

Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun aika wasiƙa zuwa ga shugabannin gargajiya da malamai a yankin, inda suka buƙaci a tara tsabar kuɗi har naira miliyan 100 kafin a fara kowanne irin wa’azi, kuma muddin ba haka ba, za su fuskanci hari na ba-zata.

Wasiƙar ta ƙunshi barazana mai tsanani, inda aka gargaɗi duk wanda ya bijire wa umarnin da hukunci mai tsauri zai biyo baya.

“Kar a ɗauki wannan saƙo da wasa. Dole ne ku biya mu Naira miliyan 100. Idan kuka ƙi, za ku fuskanci sakamakon abin da zai biyo baya, kuma babu wanda za ku zarga face kanku. Ko da kun kira sojoji ma, ba za su iya hana mu ba,” in ji wasiƙar.

Wasiƙar ta kuma yi ishara da wani hari da aka kai wa al’ummar Woro a Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, inda aka ruwaito cewa mutane da dama sun rasa rayukansu bayan an yi watsi da irin wannan gargaɗi a baya.

Wannan barazana na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da ƙaruwar hare-haren ’an ta’adda a wasu sassan jihar, musamman bayan wani hari da ake zargin ƙungiyar Lakurawa ta kai a Ƙaramar Hukumar Kangiwa, inda aka ce an kashe mutane fiye da 30.

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce hankalin jama’a ya tashi ƙwarai, lamarin da ya sa har malamai suka shiga fargabar ko za su iya fitowa su yi wa’azi a wannan watan mai alfarma.

“Yanzu mutane na cikin tsoro, ba wanda ya san abin da zai faru idan aka bijire wa umarnin ’yan bindigar” in ji shi.

Da yake tabbatar da sahihancin wasiƙar, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakai cikin gaggawa domin daƙile duk wata barazanar kawo hari.

A cewarsa, tuni dai Gwamna Nasir Idris, ya bayar da umarnin tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa, domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

A al’ada, watan Ramadana lokaci ne da ake gudanar da Tafsiri da wa’azuzzuka daban-daban domin ƙara kusantar jama’a da addininsu.

Sai dai wannan sabon lamari ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba da rashin tabbas kan yadda za a gudanar da ibadar watan cikin kwanciyar hankali.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *