Jihohi Sun Samu Kudade Daga Gwamnatin Tinubu Fiye Da Duk Wani Lokaci A Tarihi – Abdulaziz Abdulaziz (2)

[ad_1]

… a ci gaba da hirar da Editanmu Bello Hamza ya yi da mai ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara a bangare harkar jarida Abdulazizs Abdulazizs ya bayyana cewa gwamnonin kasar sun samu7 kudaden shiga daha gwamantin tarayya fiye da yadda aka samu samu a shekaru8n baya, wanda haka y6a basu damar gudanar da ayyukan raya nkasa masu dinbin yawa. Haka kuma duk da dimbim matsalolin rashin tsaro da gwamnatinsa ta gada daga gwamnatocin baya, Shugaba Tinubu ya yi rawar gani wajen shawo kan lamarin. Haka kuma ya yi bayanin yadda gwamantin Tinjubu ta farfado da ayyukan da gwamnatocin baya suka yi watsi da su musamman abin da ya shafi manyan hanyoyi a arewacin kasar nan. Ga dai yadda hirar ta kasance.

Don a kan ce wasu jihohin ma abin da suka karba a cikin shekaru biyun nan da doriya, ya nunka kusan abin da wasu jihohin suka karba cikin shekaru takwas.

Kwarai kuwa. Sosai! A jihohi da dama haka abin yake, shiyasa nake fada ai cewa ko hisabi ma za a yi, maganar gaskiya idan za a kyautata aikin da wani gwamna ya yi ko wata gwamnati ta yi a shekara hudu ko a shekara takwas, a ce za a hada da wannan shekara biyun; ai abin ba daya ba ne. Saboda kudaden da aka samu ba kadan ba ne.

Amma ba a ganin darajar kudin, misali; ayyukan da kudaden za su yi maka a wadancan shekarun, a yanzu watakila sai an kwatanta da na yanzu; duk da yawan kudin?

Ai ‘inflation’ din ya ragu. Akwai lokacin da aka samu matsalar cewa ai kudin ga yawan su, amma darajar ta ragu sosai. Amma yanzu ai darajar kudin ta sake dawowa daidai misali. Ba zance daidai yake ba, gaskiya. Da gaske ne ba daidai yake ba, tun da a wancan lokacin dala tana dari shida da wani abu, amma yanzu tana dubu daya da wani abu, amma ai yawancin abubuwan da muke yi ba na dala ba ne. Yanzu misali ma’aikata da ake dauka ai albashin an kara, amma ba nunkawa aka yi ba. Kuma albashin ma’aikatan idan a da kudin da gwamnati take biya na albashi a wata biliyan biyar ne misali a Kano, to ai yanzu ba wani bambanci ya yi sosai ba, kuma ana biya din, kuma har ana kara daukar ma’aikata.

Duk wannan wani abu ne da yake nuna cewa wato ‘financial engineering’ ne da ake fada a turance; wato sauya fasalin tattalin arzikin Nijeriya da gwamantin Bola Tinbu take yi, yana haifar da da mai ido kwarai da gaske.

Idan ka duba bangaren masu shigo da kudade daga kasashen waje domin su saka jari, ta nan ne ma babban hanyar ma da za ka dubi ci gaban tattalin arzikin. Saboda idan tattalin arzikin ka ba ya yin kyau, ba wanda zai zo. Saboda dan kasuwa ba mai sadaka ba ne, ko mai yin abu saboda Allah. Ba fisabilillah ba. Kasuwanci ne ana yi don riba. Duk wanda zai zo ya saka kudi, yana duba ta ya ya ne zai samu tasiri ya samu alheri daga wannan kudin da ya zuba. To yanzu muna ta samun karuwar sanya hannun jari da ake saukowa; kudade ana ta shigo da su za a kafa kamfani a nan, a’a za a zo a yi abin wutar lantarki, za a zo a yi railway da sauran su. Saboda sun ga cewa tattalin arzikin Nijeriya yana kyau ne.

Yanzu harkar hako mai, da sai da ya zama kamfanukan hakar mai suna ta barin Nijeriya, yanzu kuma suna ta kokarin dawowa ne. Akwai kamfanoni akalla guda biyu zuwa uku, manyan kamfanoni ne wanda a da sun fita ne, yanzu suna rokon za su dawo su ci gaba. Wasun su ma sun dawo.

Daga bayananka duk da ka fadada abubuwa ne da za a iya cewa kusan kafatanin ‘yan Nijeriya na iya ribatar su. Ka yi bayanin wasu kebantattun ayyuka da al’ummar yankin arewa suka amfana; hanyoyi da layin iskar gas da ake janyowa. Amma tattare da hakan, mutanen yankin na ganin an fi karkata ribar da kasar ke ciki ga bangaren Kudanci, watakila saboda shi shugaban kasar daga can ya fito, ko kuma wani abu mai kama da haka.

Wato lokacin da gwamnatin nan ta zo kusan ayyukan more rayuwa da yawa ana gudanar da su a arewacin Nijeriya. Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayar da ayyuka. Wadanda wasun su ba a ma fara ba, ko kuma ana kokarin fara su, ko kuma ba a dade da farawa. A Kudu yawanci babu irin wadannan ayyukan. Idan banda idan ka dauki hanyar Legas – Ibadan da kuma wancan gadar da take hada kasar Inyamurai – gabashi da kudancin Nijeriya, wato ‘East-West Road second Niger Bridge’, idan banda wannan wanda yawancin su an gama su ko ana tunanin kammala wa. Amma a nan arewa, nan aka zo aka tarar da ayyuka da yawa, wanda ayyuka ne na kudade masu yawan gaske. Kamar yadda na ce an bayar da su, amma aikin ba su je ko’ina ba. Amma gwamnatin nan ta ci gaba da su.

Abin da mutane suke so shi ne kullum a ce an bayar da aiki a nan kaza, an bayar da aiki a nan kaza. Amma babban abu mafi muhimmanci ga shugaba mai adalci, mai tunani shi ne ya karasa aikin alherin da ya tarar an fara. Ba wai aikin da zai ba shi suna ba, a ce ai shi ya fara wannan aikin.

Mu ba mu damu a ce ai Buhari ne ya fara aikin Kano zuwa Kaduna ba da Abuja ba, ba damuwa. Mu wannan gwamnatin tana son ta ga ta kammala. Idan da wannan gwamnatin tana da niyyar, tana da manakisa tana da niyyar keta, ga arewacin Nijeriya, wadannan ayyuka da dama da muka tarar sai mu bar su, sai a ki kammala su, sai a yi rikon sakainar kashi, sai a yi wassarere, a bar su.

Ka tuna akwai ayyukan da sun fi shekara ashirin ana yin su, misali; titin Abuja zuwa Lokoja, ko titin Kano zuwa Maiduguri. An yi shekaru, wasu tun Obasanjo, wasu tun ‘Yar’adua.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa inshaAllah

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *