Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere
[ad_1]
Yundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta tabbatar da cewa ɗaya daga cikin ’yan mata 14 da ƙungiyar ISWAP ta sace a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba ta kuɓuta, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano sauran 13.
A sanarwar da ya fitar dangane da irin ƙoƙarin da Jami’an tsaron ke yi na ceto sauran ‘yan matan 13 da ke hannun ‘yan ta’addan, kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce, shugaban gundumar Huyum ya bayar da rahoto a ranar Asabar 22 ga Nuwamba cewa waxanda ake zargin mayaƙan Ƙungiyar ISWAP ne suka sace ‘yan matan, yayin da suke aiki a wata gona a gundumar Mussa.
Tawagar ’yan sanda, sojoji, Sibiliyan JTF, da mafarauta da ’yan banga nan da nan suka fara aikin bincike don ceto ’yan matan.
“Ɗaya daga cikin waxanda abin ya shafa ta tsira ba tare da wata matsala ba a lokacin aikin kuma an ceto ta,” in ji Daso.
Ya ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Naziru Abdulmajid, ya yi kira ga mazauna yankin da su kasance masu lura yayin da hukumomin tsaro ke ƙara himma wajen ƙoƙarin ceto sauran ‘yan matan.
Sanarwar ta ce, “Ana shawartar manoma da mazauna yankin da su yi aiki a yankunan da jami’an tsaro ke sintiri,” in ji sanarwar.
Rundunar ta ce za a samar da ƙarin bayani yayin da ake ci gaba da aikin gano wurin da waɗannan mata suke.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link