Gwamnatin Kebbi ta sake jaddada goyon bayanta ga hukumomin tsaro

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Kebbi ta sake jaddada ƙudirinta na ci gaba da tallafawa dukkan hukumomin tsaro da ke yaƙar ’yan bindiga da ta’addanci a jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na Jihar, Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya tarbi Daraktan Yaɗa Labaran Sojoji, Birgediya Janar T. I. Gusau, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Birnin Kebbi.

Alhaji Yakubu ya bayyana irin muhimman tallafin da Gwamna Nasir Idris ke bayarwa tun daga lokacin da ya fara mulki shekaru biyu da suka gabata, wanda ya haɗa da kayayyakin aiki da alawus da kuma bayanan sirri ga jami’an tsaro.

Ya ce, gwamnatin za ta ci gaba da ɗaukar nauyi domin ƙara ƙarfafa ƙoƙarin yaƙi da ’yan bindiga.

Ya kuma shawarci hidikwatar tsaro da ta shirya taron tattaunawa tare da manyan masu ruwa da tsaki kamar sarakunan gargajiya da shugabannin addini da shugabannin al’umma da ƙungiyoyin matasa domin samar da haɗin kai da zai taimaka wajen samar da bayanan sirri ga jami’an tsaro.

Kwamishina ya ƙara da cewa, ma’aikatarsa a shirye take ta yi aiki tare da sashen yaɗa labaran sojoji wajen shirya wannan taro, domin amfani da tasirin shugabannin gargajiya wajen samun goyon bayan jama’a.

A nasa jawabin, Birgediya Janar Gusau ya shaida wa Kwamishinan cewa, ya zo jihar tare da tawagarsa domin ganin tasirin haɗin gwiwar da suka shiga da wasu kafafen yaɗa labarai, wanda manufarsa ita ce ƙarfafa dangantaka tsakanin sojoji da al’umma wajen yaƙi da ’yan bindiga a Jihar Kebbi da ma Arewa maso Yamma baki ɗaya.

Ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da jama’a a dukkan wuraren da ake yaƙi da miyagun laifuka.

Haka kuma, ya yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa irin goyon bayan da yake bayarwa ga rundunar sojoji, yana mai cewa hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da aka samu har zuwa yanzu.

Birgediya Janar Gusau ya kuma isar da saƙon godiyar babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, ga Gwamnatin Jihar Kebbi bisa jajircewarta wajen ganin an dawo da zaman lafiya a Jihar Kebbi musamman da kuma yankin Arewa maso Yamma baki ɗaya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *