’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja

[ad_1]



Aƙalla mutum huɗu suka rasu yayin da aka sace wasu tara a wani hari da ’yan bindiga suka kai a ƙauyuka da dama na Ƙaramar Hukumar Magama; ciki har da garin Ibeto a Jihar Neja.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa mutum huɗu aka kashe, an jikkata wasu 11, sannan an yi garkuwa da mutum tara.

Daga cikin waɗanda aka sace har da wanda ya wallafa rubutu a Facebook kan hare-haren ’yan bindiga a yankin, Barista Isyaku Muhammad Danjuma.

Rahotanni sun nuna cewa wasu masu bai wa ’yan bindiga bayanai ne suka sanar da su halin da ake ciki a yankin.

Mazauna yankin sun ce ’yan bindigar ɗauke da makamai sun kwana a Ibeto, inda suka dinga shiga gida-gida suna harbi tare da yin garkuwa da mutane.

Manoma da dama sun tsere daga gidajensu bayan harin, inda suka fantsama zuwa wasu ƙauyuka na Magama.

Hakazalika, ’yan bindigar sun sace shanun jama’a da dama daga daren ranar Talata zuwa ranar Laraba.

A wani bidiyo da ta karaɗe kafafen sada zumunta, an hangi maharan su suna kaɗa shanu daga garin Ibeto.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ci tura, domin bai ɗaga kiran waya ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *