Jagoranci Mai Ban Mamaki: Harkokin Shugabancin Babban Sakatare Xi Na 2025
[ad_1]
Shekarar 2025, wadda muka yi ban kwana da ita, shekara ce mai ban mamaki. A karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin tare da kwamared Xi Jinping a matsayin babban jagora, al’ummomin dukkan kabilu a kasar Sin sun shawo kan matsaloli kuma suka yi aiki tukuru don cimma manyan manufofin ci gaban tattalin arziki da zamantakewa, inda suke bin matakai ba tare da tangarda ba a kan sabuwar hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. “Babban jirgin ruwan kasar Sin” ya yi tafiya cikin sauki da kwanciyar hankali a kan hanyarsa ta zuwa wurin da ya nufa.
A ranar 1 ga Janairun 2026, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya kaddamar da wani shiri na musamman, mai taken “Jagora mai ban mamaki: jerin harkokin shugabancin babban sakatare Xi Jinping a kasar Sin na shekarar 2025,” wanda ya kunshi shirye-shirye guda biyu. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link