Sin Ta Samu Karuwar Kashi 20 Na Balaguro Tsakanin Yankuna A Ranar Farko Ta Hutun Sabuwar Shekara

[ad_1]

An samu balaguron fasinjoji miliyan 207 a tsakanin yankunan kasar Sin a ranar farko ta hutun sabuwar shekara na tsawon kwanaki uku, watau a jiya Alhamis, inda adadin ya karu da kashi 20.3 cikin dari a mizanin shekara-shekara, kamar yadda bayanai daga ma’aikatar sufuri ta kasar suka nuna a yau Jumma’a.

Tafiye-tafiyen titunan mota su ne suka fi yawan fasinjoji, inda aka samu adadin balaguro miliyan 186.28 wanda ya karu da kashi 17.5 cikin dari idan an kwatanta da na shekarar da ta gabata.

Yawan balaguron fasinjojin da suka bi sufurin jirgin kasa kuma ya kai jimillar miliyan 18.56, wanda ya karu da kashi 67.9 cikin dari a mizanin shekara-shekara. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *