An kashe ɗan shekara 13 da shanu 36 a wani sabon hari a Filato
An kashe wani yaro ɗan shekara 13 mai suna Abubakar Wada da shanu 36, yayin da wasu ’yan bindiga sun kai wa makiyaya hari a kusa da ƙauyen Inzon da ke yankin Fan, a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato.
Aƙalla shanu 49 kuma sun ɓace ba tare da sanin inda suka shiga ba.
Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya bayyana cewa harin ya faru ne da yammacin ranar Talata lokacin da wasu makiyaya uku ke dawowa daga kiwo.
Ya ce ’yan bindigar sun buɗe wa dabbobin wuta, tare da kashe yaron wanda makiyayi ne, yayin da sauran biyun suka tsallake rijiya da baya.
Babayo ya ce: “Mun yi asarar sama da shanu 80, saboda 36 an kashe su, yayin da 49 suka ɓace. Mun gano cewa maharan Berom ne daga yankin Fan.
“Wannan abu ne mai ban tsoro da rashin imani. Makiyayan suna tafiya lafiya ba tare da sun tayar da hankali ba.”
Ya buƙaci makiyaya a faɗin jihar su kwantar da hankalinsu, su bar jami’an tsaro su gudanar da bincike, inda ya yi gargaɗin ɗaukar doka a hannu.
Sakataren MACBAN a Barkin Ladi ya tabbatar da cewa dukkanin hukumomin tsaro sun samu rahoton harin, inda jami’an Operation Enduring Peace, DPO na Barkin Ladi suka ziyarci wajen da harin ya auku.
Ya ƙara da cewa a ranar Lahadin da ta gabata, an kashe shanu guda biyar a wannan yankin kuma matasan Berom ake zargi.
Matasan Berom sun musanta zargin
Shugaban ƙungiyar matasan Berom (BYM), Barista Solomon Dalyop, ya musanta zargin, inda ya bayyana cewa mutanen Berom masu ƙauanar zaman lafiya ne.
Ya ce: “Waɗannan zarge-zargen kawai wata hanya ce ta neman dalilin kai wa mutanenmu hari.
“A gaskiya, an kai hare-hare guda biyu ta hannun wasu da ake zargin Fulani ne a ranar 6 ga watan Oktoba, 2025 da misalin ƙarfe 7:30 na yamma, inda aka kashe wani mutum mai suna Timothy Ishaku Chollom.”
Dalyop, ya ƙara da cewa ci gaba da kiwo a gonaki da wuraren zama yana tayar da hankali, kuma yana barazana ga rayuka a yankin Fan.
Sojoji sun fara bincike
Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojojin Najeriya Sashe na 3, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce rundunar sojin ta fara bincike kan lamarin.
Ya ƙara da cewa sun tuntuɓi kwamandan sashen da ke yankin domin tabbatar da bayanai game da harin.