Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika

[ad_1]


An bude babban taron kungiyar kawancen habaka amfani da kimiyya da fasaha a aikin gona ta Sin da Afirka, na shekarar 2025 jiya Litinin a Addis Ababa, babban birnin Habasha, inda aka mayar da hankali kan hadin gwiwar samun wadatar abinci da zamanantar da aikin gona a Afirka.

Batun zamanantar da aikin gona da ma wadatar abinci, muhimman batutuwa ne dake zama manyan kalubalen da nahiyar Afrika ke fama da su, ganin yadda ake fama da yunwa da rashin fasahohin zamani a bangaren aikin gona a nahiyar.

Sauyin yanayin, rashin tabbas a duniya, da ma tashe-tashen hankula na ci gaba da yin mummunan tasiri ga aikin gona da wadatar abinci a nahiyar Afrika, duk da cewa nahiyar ce ke da kaso 60 na kasar noma a duniya.

Idan muka kwatanta da kasar Sin, sabanin yawan albarkatun da Afrika ke da su kamar na kasar noma, ita Sin kasa da kaso 9 kadai take da shi, amma kuma tana bayar da gagagrumar gudunmawa a duniya, inda take tsaye da kafarta wajen ciyar da al’ummarta, har ma ta bayar da gudunmawa ga kasashe mabukata.

To mene ne dalilin nasarar Sin a wannan bangare?

Gaggarumar nasarar da Sin ta samu a bangaren aikin gona, ba wani abu ba ne illa jajircewar gwamnatin kasar da dabaru da fasahohin aikin gona da kullum ake lalubowa. Misali, ko a cikin hamada, kasar Sin ta lalubo dabarun da suka dace, inda ake noman tsirrai masu juriya dake iya ciyar da mutane da samar da kudin shiga tare da yaki da kwararar hamada. Haka kuma, fasahohinta na samar da ingantattun iri da noma cikin daki ko rumfa, duk abubuwa ne da suka bunkasa yabanya a kasar. Ga uwa uba kayayyakin aiki na zamani da manomanta ke amfani da su. Za mu iya bayyana aikin gona a kasar Sin a matsayin wata sana’a ta zamani sabanin yadda ake ganinta a matsayin sana’a mai wahala da bata samar da kudin shiga.

La’akari da yawan jama’a da yadda ta kasance koma baya, tabbas nahiyar Afrika na bukatar fasahohin Sin domin fitar da al’ummominta daga kangin talauci tare da wadatar da su da abinci. Dabaru da fasahohin Sin, za su yi wa bangaren aikin gona a nahiyar gagarumin garambawul, domin idan aka tabbatar da hada fasahohin da tarin albarkatun da nahiyar take da su, to kasashen Afrika za su iya tsayawa da kafarsu, su kuma fatattaki yunwa da talauci, da karfafa gwiwar matasa ta yadda za su rika ganin aikin gona a matsayin wata sana’a mai riba. Tabbas ingantattun fasahohin aikin gona na Sin, za su taka rawar gani wajen kyautata makomar nahiyar Afrika. (Fa’iza Mustapha)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *