Yawan Fasinjojin Da Jiragen Kasa Suka Yi Jigilarsu a Kasar Sin Ya Zarce Biliyan 4.5 A Shekarar 2025
[ad_1]
A shekarar 2025 da ta gabata, yawan fasinjojin da jiragen kasa suka yi jigilarsu a kasar Sin ya kai biliyan 4.588, adadin da ya karu da kaso 6.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabaci hakan, kana yawan kayayyaki da hajojin da aka yi jigila cikin jiragen kasa ya kai tan biliyan 5.273, wanda ya nuna karuwar kaso 2.0 bisa dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabace ta.
Hukumar lura da sufurin jiragen kasa ta kasar Sin ce ta bayyana hakan a gun wani taro da aka gudanar a yau Alhamis, dangane da zirga-zirgar jiragen kasa na kasar na shekarar 2026.
A yayin zaman, daraktan hukumar Song Xiude, ya bayyana cewa, a lokacin gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, tsayin layukan dogon jiragen kasa a Sin ya kai kilomita dubu 165, kuma cikin adadin, tsayin layukan dogo na jiragen kasa masu saurin tafiya ya zarce kilomita dubu 50. Kazalika, yawan zirga-zigar fasinjoji da dakon kayayyaki, da zirga-zirgar hajoji da kuma ingancin sufuri, dukkansu sun kai matsayin farko a duniya.
Jami’in ya kara da cewa, “Tsarin manyan ababen more rayuwa masu nasaba da jiragen kasa na zamani yana ci gaba da samun kyautatuwa, lamarin da ya kara nuna goyon baya mai karfi ga bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’umma.” (Amina Xu)
[ad_2]
Source link