Majalisar Dokokin Legas Ta Amince Da Kasafin Tiriliyan ₦4.4 Na Shekarar 2026
[ad_1]
Majalisar Dokokin Jihar Legas ta amince da jimillar kasafin kuɗi na Tiriliyan ₦4.4 domin gudanar da harkokin jihar a shekarar 2026. An amince da kasafin ne a zaman majalisa da aka gudanar a ranar Alhamis, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Mudashiru Obasa, inda aka zartar da ƙudirin kasafin kuɗin ya zama doka.
Shugaban Kwamitin Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi da Kasafi na Majalisar, Hon. Olumoh Sa’ad, ya bayyana cewa kasafin da aka amince da shi ya ƙunshi ₦2.1 tiriliyan domin kashe-kashen yau da kullum, yayin da aka ware ₦2.33 tiriliyan don manyan ayyukan raya kasa. Kasafin zai kai wajen aiwatar da ayyukan gwamnati har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2026.
- Mutum Biyu Sun Mutu Yayin Da Tankar Mai Ta Kama Da Wuta A Titin Legas
- Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legas
Bayan amincewa da kasafin, Kakakin Majalisar ya umurci Magatakardar Majalisar, Olalekan Onafeko, da ya miƙa kwafin kasafin da aka gyara ga Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, domin sanya hannu ya zama doka. Tun a baya, a ranar 25 ga Nuwamba, 2025, gwamnan ya gabatar da kasafin kuɗin ₦4.237 tiriliyan ga Majalisar, wanda ya sanya wa suna “Kasafin Ci Gaban Bai Daya.”
Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana cewa manufar kasafin ita ce bunƙasa tattalin arziƙi mai haɗa kowa da kowa tare da inganta walwalar al’ummar jihar. Ya ce tsarin kashe-kashen ya ta’allaƙa ne kan ginshiƙai huɗu: mayar da hankali kan jin daɗin al’umma, da gina ingantattun ababen more rayuwa, da bunƙasar tattalin arziki, da nagartacciyar shugabanci, bisa tsarin ajandar T.H.E.M.E.S+ ta jihar.
[ad_2]
Source link