Dalilin da na koma jam’iyyar APC — Gwamnan Zamfara

[ad_1]



Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce rikicin cikin gida da kuma taƙaddamar shari’a da ke addabar jam’iyyar PDP su ne manyan dalilan da suka sa ya fice daga jam’iyyar zuwa APC.

Mataimakin gwamnan jihar, Mani Mummuni, ne ya sanar da sauya shekar a hukumance ranar Litinin bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Gusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce matakin komawa Jam’iyyar APC ya zama dole domin ci gaba da bunƙasa al’umma da kuma kare muradun Jihar Zamfara.

Sanarwar ta ce shawarar sauya sheƙar ta biyo bayan matsalolin shari’a da rikicin cikin gida da PDP ke fuskanta, wanda ya haddasa jerin ƙalubale da ka iya shafar shirye-shiryen jam’iyyar a zaɓukan shekarar 2027.

Sanarwar ta ƙara da cewa Gwamna Dauda Lawal ya yi ƙoƙari wajen sasanta ɓangarorin jam’iyyar domin a samu haɗin kai, amma ƙoƙarin samar da sulhu ba tare da zuwa kotu ba bai yi nasara ba.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnan ya yanke hukuncin sauya sheƙar ne bayan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta yanke ranar Litinin, wanda ya tabbatar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta hana Hukumar Zaɓe (INEC) amincewa da sakamakon babban taron jam’iyyar PDP na ƙasa da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo.

A cewar sanarwar, gwamnan ya shiga APC ne domin ci gaba da aiwatar da shirinsa na “Ceto da Sake Gina Zamfara” tare da fifita muradun al’ummar jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *