Matasa Biyu Sun Afka Tafkin Ruwa Yayin Tserewa Masu Ƙwacen Waya A Kano

[ad_1]

Matasa biyu sun rasa rayukansu a jihar Kano bayan sun faɗa cikin wani tafki yayin da suke kokarin tserewa wasu da ake zargin masu kwacen waya ne.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce abin ya faru ne ranar Juma’a, 6 ga Maris, 2026, a Ring Road Kureken Sani da ke karamar hukumar Kumbotso.

  • APC Na Da Gwamnoni 31 Bayan Sauya Sheƙar Gwamnan Zamfara
  • Kotu Ta Ci Tarar Gwamnatin Kano Miliyan 1 A Shari’arta Da Tsofaffin Kwamishinoni

Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce wadanda suka rasun sune Sadiq Isyaku mai shekaru 18 da Auwal Isyaku.

Ya bayyana cewa an tsamo su daga cikin tafkin a sume, amma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu.

A cewarsa, an miƙa gawarwakinsu ga mahaifinsu, Ibrahim Shehu, mazaunin Unguwa Uku.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *