2027: Dalilin da ya sa Atiku bai ayyana takararsa ba — Hadimi
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, har yanzu bai ayyana cewa ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba.
Yayin da wasu ’yan siyasa kamar Peter Obi da Rotimi Amaechi suka nuna sha’awar tsayawa takara, Atiku ya ce “lokaci bai yi ba” domin yanke hukunci.
Kwanan nan, wasu rahotanni sun bayyana cewa Atiku ya faɗa wa BBC Hausa cewa zai bai wa matashi damar tsayawa takara.
Wannan ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta.
Amma hadiminsa, Paul Ibe, ya ce ba a yi wa maganganun Atiku kallo na tsanaki ba, an fahimce su ba daidai ba.
Ibe, ya bayyana cewa Atiku yana nufin zai girmama tare da goyon bayan duk wani matashi da ya kayar da shi a zaɓen fidda gwani.
Ya jaddada cewa Atiku bai taɓa cewa zai janye wa kowa ba.
A cewar Ibe, Atiku yanzu ya mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwar jam’iyyar ADC.
Ya ce Atiku na halartar taruka tare da sauran manyan ’yan siyasa, kuma yana bayar da gundumawa don ganin sun yi nasara a zaɓen 2027.
Ya kuma ce Atiku na ganin cewa abin da ’yan Najeriya suka fi buƙata shi ne shugabanci na gari, ba batun yanki ko asalin ɗan takara ba.
A cewarsa abin da ya fi muhimmanci a yanzu, shi ne samun shugaba mai ƙwarewa da zai magance matsalolin ƙasa.
Atiku, ta bakin hadiminsa, ya yi kira ga matasa da mata da su shiga harkar siyasa sosai.
Ya yi alƙawarin cewa haɗin gwiwar zai bai wa matasa da mata muhimmiyar dama wajen tsara makomar Najeriya.
Ibe, ya ƙara bayyana Atiku a matsayin ɗan siyasa na gari wanda zai amince a yi takara ta gaskiya.
Ya ce Atiku ba zai taɓa hana kowa tsayawa takara ba, domin shi ma zai fita filin zaɓe ya gwada farin jininsa.