AFCON 2025: Nijeriya Ta Kai Matakin Kusa Da Na Ƙarshe Bayan Doke Algeria

[ad_1]

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin na kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin ƙasashen nahiyar Afirika, bayan ta doke ƙasar Algeria da ci 2 da nema a filin wasa na Grande Stade dake birnin Marrakesh.

Wasan wanda aka buga da misalin ƙarfe 5 na yamma agogon Nijeriya, ya matuƙar ɗaukar hankalin masu kallon ƙwallon ƙafa a nahiyar Afirika, duba da cewa duka ƙasashen biyu babu na rainawa a fagen taka leda.

  • Wang Yi Ya Gabatar Da Shawarwarin Kara Zurfafa Kawancen Sin Da Afirka
  • Hukumar NDLEA Ta Kama Mutum 1,130 Da Kwato Miyagun Kwayoyi Kilo 9,402 A 2025 A Kaduna

Duk da cewar an buga mintuna 45 na farkon wasan ba tare da ci ba, Nijeriya ta jefa ƙwallonta ta farko minti 2 da dawowa daga hutun rabin lokaci ta hannun Victor Osimhen.

Ƙwallo ta biyu da Nijeriya ta jefa a wasan ta fito ne ta hannun Akor Adams bayan ya yanke mai tsaron raga Enzo Zidane cikin ƙwarewa kafin ya zura kwallon cikin raga.

Da wannan nasarar da Nijeriya ta samu, ƙasar za ta buga wasan kusa da na ƙarshe tsakaninta da masu masaukin baƙi wato Morocco a ranar Laraba mai zuwa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *