2027: Ana Zazzafar Muhawara Kan Muslim-muslim Tiket A Takarar Tinubu

[ad_1]

Masu tsara dabarun siyasa na arewa da ra’ayoyin shugabannin sun cire yiwuwar ɗaukar Bishop Mathew Hassan Kukah, a matsayin mai yiwuwa ya maye gurbin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a zaven 2027.

Wani yunƙuri na baya-bayan nan, wanda ake cewa Amurka ta tayar, ya tayar da zazzafar da muhawara game da tikitin Musulmi-Musulmi da Shugaba ƙasa, Bola Tinubu ya yi amfani da shi a zaven 2023.

Shugaba Tinubu ya yi takara da Sanata Shettima a cikin tsarin Musulmi-Musulmi tiket, wanda wasu shugabannin Kiristoci a ƙasar suka yi adawa da shi.

Amma adawar ta ɗan ragu bayan manyan kamfen-kamfen da suka jaddada halayen Tinubu na juriya ga addini da kuma zaman lafiya na addinai da ke akwai a yamma maso kudu, inda ya fito.

  • Babban Taron APC: Ƙungiyar Masu Ruwa Da Tsaki Ta Amince Da Yilwatda
  • 2027: Atiku Ya Gargaɗi Magoya Bayansa Kan Tsangwamar Jama’ar Peter Obi

Duk da haka, rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump ta Amurka ta yi imani cewa ƙasar na buƙatar alamar haɗin kai na addini ba kawai a yankin yamma maso kudu ba, har ma a kowai vangare na ƙasar.

Ko da yake wata majiya a arewa ta ce Amurka na iya neman daidaito na addini don voye ainihin manufofinta a Nijeriya, an gano cewa shugabannin siyasa na arewa san yi watsi da tattaunawar tare da cikakken bincike ba.

Daga cikin sunayen Kiristoci uku da suka fito kwanan nan a matsayin yiwuwar ‘yan takara don daidaiton addini, an samu labarin cewa masu ruwa da tsaki a arewa sun yi watsi da yiwuwar takarar Bishop Kukah, yayin da wasu masana a arewa suka ce an sanya masa laƙabi da yana cikin siyasa sosai.

An ruwaito cewa ba saboda ya tava riƙe mukamin siyasa ba ne aka kawo wannan lamari, amma wani bayani ne kan rawar da ya taka a kwamitin zaman lafiya na ƙasa da kuma yadda yake bayyana ra’ayinsa kan al’amuran ƙasa.

Majiyar ta bayyana cewa an riga an ɗauki bishop a matsayin ɗan siyasa kuma sanya shi a muƙamin siyasa na iya rage gudunmawarsa ga ƙasa.

Bayan wannan mataki na Amurka da aka ambata, an tattara cewa wasu sunaye ban da na Bishop Kukah an yi nazari a kansu ga jiga-jigan siyasa a arewa. Sunayen sun haɗa da ministan tsaro, Janar Christopher Musa, da kuma shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda.

Wani majiya ta ce, “Bishop Kukah na iya kasa yin aiki yadda ya kamata, saboda wasu masu sharhi suna ganin shi a matsayi mai tuzarta siyasa kuma hakan ya fi faruwa saboda rawar da ya taka a rayuwarsa zuwa yanzu. Janar Musa ba a bayyana shi haka ba. Ya yi aikin sojoji, kuma yanzu shi minista ne.

“An haife shi a Jihar Sakwato kuma ba a gan shi a matsayin mutum mai matsala. Yayi da shi kuma Farfesa Yilwatda ya kasace kammalallen mutum. Kwanaki kaɗan da ya bayyana a fagen siyasa, amma kamar Musa, bai yi fice a vangare siyasa ba.”

An bayyana cewa ko kafin sabon yunƙuri na daidaita addini a ofishin shugaban ƙasa, tun wasu watanni da suka gabata ƴan arewa sun riga sun fara dubawa a cikin ‘yan takarar da ake sa ran za a ba da shawarar su maye gurbin mataimakin shugaban ƙasa.

Idan za a iya tunawa dai, batun rabuwar takara tsakanin Tinubu da Shettima a 2027 ya kasance a kan tebur fiye da shekara guda da ta wuce. Aƙalla sunaye shida ne suka fara bayyana a tattaunawar maye gurbin Shettima, kafin a sami sabon matsin lamba daga Amurka.

Majiyoyi sun ce wasu shugabanni a faɗin ƙasar ma suna nazarin yiwuwar daidaito na addini a cikin majalisar Tinubu don rage irin tashin hankali da aka ƙirƙiro kafin zaven 2023.

Wasu daga cikin sunayen da suka bayyana sun haɗa da tsohon shugaban jam’iyyar APC, Dakta Umar Abdullahi Ganduje da tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, da tsohon gwamnan Jihar Kano kuma shugaban jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwakwanso.

Sauran sun haɗa da shugaban majalisar wakilai, Hon Tajudeen Abbas da tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da mashawarci na tsaron ƙasa, Malam Nuhu Ribadu.

Sai dai an samu labari cewa ƙungiyar masu nazarin siyasa tana da ra’ayin cewa idan shugaban ƙasa na son naɗa Kirista a matsayin wanda zai maye gurbin Shettima, ya zavi Dogara, yayin da sauran ‘yan takara ma an bincika su wajen sanin ƙarfinsu da rauninsu.

Saoda haka, tun bayan da Amurka ta bayyana daidaito na addini kafin zaven 2027, ya bambanta bincike da matakin tattaunawa, in ji wata majiya a ƙarshen mako.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *