Nasiha Ga Masu Kudin Da Ba Sa Fidda Da Zakkah Kuma Ba Sa Taimakon ‘Yan’uwa
[ad_1]
Daga Ibrahim Bala
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Barkanmu da sake kasancewa tare da wannan fili mai albarka, filin da muke tattaunawa game da abubuwan da suke ci wa al’umma tuwo a kwaya.
A wannan gaba ina so nayi magana akan mutum biyu zuwa uku. Na farko shuwagabannin da suke sace kudin mutane, suna ganin bari su tarawa ‘ya’yansu. Na biyu masu kudin da suke tara dukiya ba sa iya yin zakkah, ba sa iya taimakon ‘yan’uwa, makota, da abokanan arziki. Na uku, ‘yan kasuwar da ba sa iya fidda zakkah, saboda kar su yi talauci, su bar ‘ya’yansu ba su samu abin da suka bari na gado ba.
Ya ilahil’alamina mu sani ita dukiya da ka ke gani arziki Allah ne yake tara shi ba wai dan’adam ba. To mu ji tsoron Allah shugabanni, idan ka mutu ranar gobe alkiyama Allah zai tsaida kai, kuma za ka zo a daure da ankwa, adalcinka shi zai kwace ka. Kuma arziki da talauci na Allah ne.
A barshi ma a matsayinka na shugaba, musamman shugabanci da aka zabi mutane matsayinsu na wakilai, aka baka kudin al’umma ka cinye, ka yi musu aiki baka yii ba, ka zo ka tara to, za ka mutu. A barshi ma ka mutum baka yi talauci ba to, ka mutu ka bar dukiyar. Kuma duk tarin girman gidanka da girman gonarka, da girman ‘guest house’ dinka a dan rami dan kankani za a saka a bunne ka.
To, ya kamata mu sani shi arziki da talauci duk na Allah ne, in Allah ya ga dama duk arzikinka gobe sai ka wayi gari ba ka da shi. Mu ji tsoron Allah amana ce dukiya, mu yi wa mutane abin da ya kamata wanda ko bayan ka mutu ya zama sadakatul jariya, abun zai rika zuwa a kabarinka.
Ga shi dai hakkin al’umma ne aka baka aka ce ka je ka yi musu, amma in ka yi din ma ya zama sadakatul-jariya za ka rika samun lada, me makon ka wawashe kudi ka tara dukiya ka je ka batar a kasashe, ko kuma kai ta siyan guri kana ginawa. Ka manta da za ka iya mutuwa lokaci daya to, wannan shi ne.
Su kuma wadanda ba sa bayar da Zakkah ‘yan kasuwa, kasani yau in Allah ya ga dama duk abin da ka tara na arziki wallahi Allah zai iya aiko da masifa kudin nan su kare. Ka fidda zakkah ka tsira a duniya, ka fidda zakkah ka tsira a lahira.
Wannan tara dukiya da ka yi ba shi zai tsirar da kai ba, in Allah ya rike maka ita babu wanda ya isa ya tarwatsa maka dukiya. Amma bin dokoki da Allah ya tsara sai ka ga ka tsira, wanda ya baka ya ce ga yadda yake so ka yi da dan wani abu daga cikin abin da ya baka, ka ce ba za ka yi ba ai kuskure ne.
Mu sani siyan gidaje da filaye ba shi yake hana talauci ba, in Allah ya ga dama rana daya sai ya tsayar da kasuwancinka ya daukaki wani. Duk wannan ya zama izna, mun saba gani hamshakin dan kasuwa ya zo ya wayi gari babu. To, mu yi adalci in lokacin Zakkah yayi mu fitar mu taimaki mutane iya irin Zakkar da aka yarda ka yi ta a musulunci ba ta wayo, ta dabara ba, kuna bayar da dubu biyu, dubu uku, wannan rashin adalci ne.
Sannan masu kudi kuma da Allah ya hore musu kudi ta wasu hanyoyi da dama da ba sa son taimako, su ma suna gudun talauci. Sai ka ce ai kai ka yi wahalarka, a’a! idan a gida ne kai Allah ya daukaka ya baiwa arziki to, jarrabawa Allah ya baka ya ga ya za ka yi. To, ‘yan’uwa mu sani cewa arziki da talauci duka na Allah ne.
Kai dai idan Allah ya baka damar to, ka yi kokari ka yi amfani da ita ta hanyar da addinin musulunci zai alfahari ko bayan mutuwarka. A yi abubuwan da ya kamata na taimako, gashi nan. Wasu saboda talauci ma da yunwa ya kan sa su aikata ba daidai ba, amma idan aka taimaka sai a ga an dawo daidai, gashinan ana bukatar ruwa gurare da yawa, ga hanya ana bukata.
Hadisi ne ingantacce in ka yi irin wannan za ka rika samun lada ko bayan rasuwarka, ubangiji Allah ka sa mu dace ka sa mu yi kyakkyawan karshe.
[ad_2]
Source link