Tawagar Jami’an Kiwon Lafiya Ta Sin Ta Tallafawa Marayu A Saliyo

[ad_1]

Tawagar jami’an kiwon lafiya ta kasar Sin ta 26, ta tallafawa wani gidan marayu dake kasar Saliyo da kayayyakin bukatun yau da kullum, albarkacin bikin shigowa sabuwar shekarar nan ta 2026, da ma burinta na kyautata ayyukan kiwon lafiya, da zamantakewar yara masu rauni dake kasar ta Saliyo.

Kayayyakin tallafin da tawagar ta gabatar ga gidan marayu dake karkashin asusun cibiyar tallafawa al’umma ta “Saint George”, dake birnin Freetown fadar mulkin Saliyo, sun hada da shinkafa, da biredi, da kayan kwalam, da na masarufi.

Yayin ziyarar mika tallafin, shugaban tawagar Liu Longfei, ya yi kyakkyawan fata ga yaran, yana mai burin ganin a nan gaba, sun zamo magadan aikin gina kasar Saliyo, kana wadanda za su gaji kyakkyawan kawancen Sin da Saliyo.

Da take karbar bakin, babbar daraktar asusun na “Saint George” Justina Zainab Conteh, ta bayyana godiyarta bisa tallafin tawagar jami’an lafiyar ta Sin da ma gwamnatin kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *