Gwamnatin Kano Ta Amince Da Ɗaukar Likitoci ‘Yan Asalin Jihar Aiki Kai-tsaye

[ad_1]

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya amince da ɗaukar ƙwararrun likitoci ‘yan asalin Jihar aiki kai-tsaye, waɗanda a halin yanzu ke aiki a wasu Jihohi, a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa samar da kiwon lafiya a faḍin jihar.

Wannan manufar na zuwa ne don magance karancin ma’aikata a manyan cibiyoyin kiwon lafiya na Kano da kuma karfafa gwiwar likitocin ‘yan asalin jihar da su komo gida don hidimtawa al’ummominsu.

  • Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Mutane 19 A Ƙauyen Katsina Da Tsakar Rana
  • EFCC Ta Kama Jarumar Kannywood, Samha Inuwa, Bisa Zargin Wulaƙanta Takardun Naira

A cikin wata sanarwa da Sakataren Gudanarwa na Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano, Mansur Mudi Nagoda, ya sanya wa hannu, kuma Mai Ba Gwamna Shawara Kan Yada Labarai, Ibrahim Adam, ya fitar, gwamnatin jihar ta ce likitocin za su shiga cikin tsarin kiwon lafiyar jihar tare da ingantattun tsare-tsaren more rayuwa da jin dadi.

“Wannan ɗaukar aikin na kai-tsaye, zai zo ne tare da cikakken aiwatar da Tsarin Albashin Lafiya na CONMESS daidai da ka’idojin tsarin gwamnatin tarayya,” in ji sanarwar.

Ta kara da cewa “likitocin za a ɗauke su akan irin matakin aiki, inda suka baro.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *