Dalilin da Ciwon Daji ke wahalar da ’yan Najeriya

[ad_1]



Yaya za ka ji a ranka, idan likita ya ce maka ka kamu da wata cuta mai haɗari ga rayuwa, wadda maganinta ke da tsananin tsada, cibiyoyin kula da ita na da matuƙar ƙaranci, ga shi kuma ba ka da kuɗi? Wannan shi ne halin da dubban ’yan Nijeriya masu fama da ciwon daji suke ciki.

Ga yawancin masu ciwon daji a Nijeriya, suna fama ne da cutar mai barazanar ɗaukar rai da kuma matsalar tsadar kuɗin jinya.

Binciken Aminiya ya nuna rashin kuɗi ya tilasta yawancin majinyatan a ƙasar sun haƙura da amfani da gamanin asibiti sun koma na gargajiya.

Yayin da Nijeriya ta da sauran ƙasashen duniya ke bikin Ranar Ciwon Daji ta Duniya ta bana, ƙasar na samun sabbin masu cutar 100,000 da kuma mutuwar 70,000 a duk shekara.

‘Yadda muke fama da cutar daji’

Wata uwa mai ’ya’ya uku daga yankin Otukpo a Jihar Binuwai, Etum Odey (ba sunanta na gaskiya ba), da ke fama da cutar ta ce an gano tana da ciwon kansar nono shekaru uku da suka gabata.

Ta bayyana cewa bayan ta lura da canje-canje a yanayin nononta, ta nemi magani a asibiti, amma daga baya ta koma ga magungunan gargajiya saboda tsadar magani.

Etum ta ce, “Na fara zuwa asibiti, amma tsadar magani ta fi ƙarfina, dole na koma shan magungunan gargajiya.”

Odey, wadda ta fara jinya a Babbar Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Makurɗi kafin a tura ta zuwa likitan ciwon daji a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Binuwai, ta ce ta kashe duk dukiyarta tana yawon neman magani tsakanin Benue, Abuja, Kaduna da Jos, ba tare da nasara ba. Yanzu tana zaune a Abuja inda ake kula da ita ta hanyar gargajiya.

Chukwueze Nnena, wacce ta tsira daga ciwon kansar mahaifa, ta ce tsadar magani ta kusan kashe ta.

“Chemotherapy na da tsada. Radiotherapy ma haka. Akwai lokacin da so in daina magani saboda rashin kuɗi.” Ta ce taimakon abokai da wata ƙungiyar agaji ne ya sa ta kammala magani.

Ronke, mai shekara 36, wacce ta tsira daga ciwon nono, ta ce lokacin da aka gano tana da ciwon daji a 2021, ta ɗauka ba za ta rayu ba.

“Na yi tunanin mutuwa zan yi. Ina da ’ya’ya ƙanana biyu, kuma abin da na fi tunani shi ne ko zan rayu har na raine su,” in ji ta.

Ta ce ta gano kumburi a nononta amma ta yi watsi da shi saboda tsoro da rashin kuɗi. Bayan ta je asibiti, likita ya ce cutar ta ci gaba. Amma bayan tiyata da chemotherapy, ta tsira. “Idan an gano da wuri, da na tsira daga wahala da yawa,” in ji ta.

Wani wanda ya tsira daga ciwon kansar mafitsara a Abuja, Orikoku Peter, ya ce an gano cutar ne a yayin da ake yi masa gwajin lafiya na yau da kullum. “Ban da wata alama. Shi ya sa dole mutane su riƙa yin gwaji akai-akai. Idan da na jira sai na ji ciwo, da yanzu ba na nan,” in ji shi.

Girman matsalar ciwon daji

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ciwon daji na daga cikin manyan dalilan mutuwa a duniya, inda ya kashe kusan mutane miliyan 10 a shekarar 2020.

A duk shekara kuma yara 400,000 ne suke kamuwa da ciwon.

A Nijeriya kuma, masana lafiya sun yi gargaɗi cewa fiye da mutum 7 cikin kowane mutum 10 masu ciwon daji na nono ana gano su ne bayan cutar ta yi nisa, sakamakon ƙarancin wayar da kai, jinkirin zuwa asibiti da kuma ƙarancin wuraren gwaji.

Shugaban Cibiyar Ciwon Daji ta Najeriya, Abidemi Omonisi, ya ce na’urar radiotherapy guda 10 kawai suke aiki a fadin ƙasar a halin yanzu.

Ya ce ƙwararrun likitocin ciwon daji a Nijeriya ba su kai 70 ba, ƙwararrun masana cututtuka kuma ba su fi 200 ba. Wannan adadi ya gaza ƙa’idar duniya, kuma yana shafar dukkan fannoni na kula da ciwon daji.

Ya ce fiye da rabin ciwon daji a Nijeriya suna Legas, abin da ya bar yawancin jihohin Arewa ba tare da samun kulawa ta musamman ba.

Matsalar rashin kayan aiki

Cibiyar Ciwon Daji ta Duniya da aka gina a kan titin Filin Jiragen Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, har yanzu ba ta fara aiki ba shekaru 16 bayan kafa ta.

Uwargidan tsohon Shugaban ƙasa, Hajiya Turai Yar’adua, ce ta fara wannan aikin a shekarar 2008 bayan ta ziyarci Cibiyar Ciwon Daji ta MD Anderson da ke Jihar Texas a ƙasar Amurka.

A 2009 ta gudanar da taron tara kuɗi inda aka yi alƙawarin Naira bilyan 6.8, amma har yanzu aikin bai fara ba.

Wakilinmu ya ziyarci cibiyar, inda ya buga ciyawa ta mamaye wurin, sai babur ɗaya kawai da aka gani. Wani mutum da ya ce ma’aikaci ne ya bayyana cewa, cibiyar “Ba ta aiki. Ban san dalili ba.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *