Da Gaske Ne Wasu Jami’ai 16 Sun Yi Yunƙurin Kifar Da Gwamnatin Tinubu — DHQ
[ad_1]
Hukumomin tsaro a Nijeriya sun tabbatar da cewa sun kama wasu jami’an soji 16 bisa zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A wata sanarwa da shalkwatar tsaro ta ƙasa ta fitar, ta ce an kama jami’an ne tun a watan Oktoban shekarar da ta gabata, bayan samun rahotannin cewa suna shirin yin juyin mulki.
- Shirye-Shiryen Cinikayya Tsakanin Sin Da Canada Ba Ta Da Nasaba Da Wata Kasa
- Shugaban Kasar Uruguay Yamandu Orsi Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Sanarwar ta ce an fara bincike a kansu ne bayan an zarge su da rashin bin doka da ƙa’idojin aikin soji.
Bayan kammala binciken, wasu daga cikin sojojin sun amince da laifin yunƙurin juyin mulki.
Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa abin da suka yi ya saɓa wa dokokin aikin soji da kuma kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Sojojin sun ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotun soji domin a yanke musu hukunci.
A baya-bayan nan, ana yawan jin jita-jitar yunƙurin juyin mulki a Nijeriya sakamakon matsin rayuwa da rikice-rikice, amma rundunar sojin ta sha musanta irin waɗannan zarge-zarge.
Nijeriya ta taɓa fuskantar juyin mulki da dama tun daga shekarar 1966 zuwa 1993.
Amma tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999, sojoji sun ce suna ɗaukar batun juyin mulki da matuƙar muhimmanci.
[ad_2]
Source link