Ina girmama sojojin Nijeriya — Wike
[ad_1]
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya musanta zargin cewa yana da wani saɓani da rundunar sojin Najeriya, yana mai cewa batun rikicin fili ne ya haɗa jami’ansa da wasu sojoji sa-in-sa da a yanzu ake faman cece-kuce a kai.
Wike ya bayyana hakan ne a yayin da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, inda ya nanata cikakkiyar girmamawar da ya ce yana yi wa sojoji, kuma babu wata gaba a tsakaninsu.
Ya ce abin da ya faru dai rikici ne da ya shafi wani mutum ɗaya mai fili da ake rigima a kai saboda mallakarsa ba bisa ka’ida ba, saboda ba rikici ba ne tsakaninsa da rundunar sojin gaba ɗaya ba.
Ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa wai yana amfani da batun filin ne don yaƙi da rundunar soji, yana mai cewa: “Ina girmama sojoji, kuma ba ni da wata matsala da su. Duk wanda yake ƙoƙarin kawo rikici tsakanina da su, kawai yana neman a rikita jama’a ne.”
A hirarsa da manema labaran, Ministan ya kuma koka kan yadda ake cin zarafin ma’aikata idan an tura su duba irin waɗannan filayen da ake zargin an mallaka ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na karya ƙa’idojin amfani da filaye ko kuma hana jami’an gwamnati gudanar da ayyukansu da ke kan ka’ida ba.
A cewar sa, babu yadda za a yi ya zauna ya yi shiru a matsayinsa na Minista alhali ana kai wa ma’aikatan gwamnati hari, “Ana dukan manyan jami’an gwamnati da suka kai matsayin darakta, ta ya za a yi su yi aikinsu bayan sun san ni ina can zaune a ofis ba zan iya kare su ba,” in ji shi.
Wike ya kuma bayar da misalin yadda wasu manyan sojoji da suka yi ritaya kamar tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo, suka samu matsalar fili, kuma su ka kira shi ya warware musu matsalar ba tare da sun tura sojoji su yi barazana ba.
Sai dai ya ce bai kamata wani ɗan ƙasa, da ya san ya yi ba daidai ba, saboda ya na da alaka da sojoji, ya hana gwamnati yin aikinta.
Rahoton ya zo ne a lokacin da ake ta tofa albarkacin baki kan takaddamar da ta barke tsakaninsa da wani matashin soja, lokacin da Wike ya je duba filin da ake zargin an mallake shi ba bisa ƙa’ida ba, inda sojan ya hana shi shiga wajen.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link