Bebejin Katsina, Alhaji Nuhu Yashe ya rasu

[ad_1]



Allah Ya yi wa Bebejin Katsina, Alhaji Nuhu Yashe, rasuwa a daren nan na Alhamis.

Wakilimu ya ruwaito, basaraken ya amsa babban kiran ne a yayin da ake gudanar da sallar Isha’i.

Kafin rasuwarsa, marigayin shi ne Hakimin Kusada, kuma suruki ne ga Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman.

Haka kuma, shi ne kakan Magajin Garin Katsina, Alhaji Aminu Abdulmuminu Kabir.

Ana sa ran za a bayyana lokacin da za a yi jana’izarsa nan gaba.

Karin bayani zai biyo baya…


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *