Sojojin Sama Sun Hallaka Fiye da Ƴan Ta’adda 40 A Borno


Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta tabbatar da kashe fiye da ƴan ta’adda 40 a hare-haren sama da aka ƙaddamar a yankunan Azir da Musarram na Jihar Borno, lamarin da ya tarwatsa shirye-shiryen hare-hare da suke shirin kai wa, tare da ƙarfafa aiyukan Sojojin ƙasa a yankin. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da jama’a na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

A cewar Ejodame, hare-haren sun gudana ne a ranakun 15 da 16 ga Janairu ta hannun ɓangaren Operation HAƊIN KAIbayan samun sahihin bayanan sirri da kuma haɗin gwuiwa da Sojojin da ke artabu a fili. Ya ce da sassafe a ranar 16 ga Janairu, jiragen NAF sun amsa kiran gaggawa a Azir, inda Sojoji ke fafatawa da ƴan ta’addan da ke ƙoƙarin janyewa daga yankin.

Bincike daga na’urar sama ya gano wasu daga cikin ƴan ta’addan suna ƙoƙarin sake taruwa a ƙarƙashin bishiyoyi a kusa, lamarin da ya sa aka ƙaddamar da jerin hare-haren saman da suka hallaka da dama daga cikinsu. Rahoton bayan harin ya tabbatar da cewa babu barazanar da ta yi saura, yayin da bayanai daga Sojoji, da hukumomin yankin da mazauna wurin suka nuna an samu kwanciyar hankali bayan raguwar ƴan ta’adda a yankin.

Tun a ranar 15 ga Janairu kuma, NAF ta kai harin sama a Musarram da ke yankin Tumbuns bayan samun bayanan sirrin cewa ƴan ta’adda na taruwa a kan jiragen ruwa domin kai hari a yankunan Baga da Fish Dam.

Jiragen sama sun hangi kusan kwale-kwale 10 ɗauke da fiye da ƴan ta’adda 40, inda aka tarwatsa su ta hanyar kai hare-hare ba’a ƙaƙƙautawa, Shugaban Sojin Sama, Air Marshal Sunday Aneke, ya jaddada aniyar NAF na ci gaba da ba da tallafin sama ga Sojojin ƙasa domin hana ƴan ta’adda samun damar sake farfaɗowa da tabbatar da tsaron yankunan da abin ya shafa.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *