Sin Ta Yi Kira Da A Himmatu Wajen Ingiza Zaman Lafiya Dangane Da Rikicin Kasar Iran
[ad_1]
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na kira ga dukkanin sassa da su yi aiki tare, bisa tafarki guda wajen samar da sahihin yanayi na gaskiya, na komawa teburin tattaunawar zaman lafiya dangane da rikicin kasar Iran.
Lin Jian, wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan, ya kara da cewa, Sin a shirye take ta ci gaba da taka rawar gani, wajen cimma nasarar wannan buri.
Kana kuma, yayin da wani dan jarida ya yi masa tambaya game da shirin shugaban Amurka Donald Trump, na gudanar da ziyara a kasar Sin, Lin ya ce diflomasiyyar shugaban kasa na taka muhimmiyar rawa, wajen wanzar da kyakkyawar alakar dake akwai tsakanin Sin da Amurka. Kuma sassan biyu suna ci gaba da tuntubar juna dangane da ziyarar ta shugaba Trump a Sin.
Har ila yau, an gabatar da tambaya dangane da rahotanni daga ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, dake cewa wani rukunin kamfanonin kirar makamai na Amurka, na shirin gina sabuwar ciniyar kera harsasai a kasar Philippines, da nufin wai taimakawa kawayen kasar da damar samarwa, da dorewar kayayyakin ayyukan soji kusa da wuraren da ake bukatar su.
Game da matsayar Sin kan wannan batu, Lin Jian ya ce Sin ta sha nanata matsayarta, cewa hadin gwiwar ayyukan soji, da tsaro tsakanin kasashe daban daban, bai kamata ya zamo domin tunkara, ko illata moriyar wata kasa ta daban ba, kana bai dace ya zamo makami na haifar da matsala ga zaman lafiya da daidaiton wani yanki ba. Ya ce kamata ya yi Amurka da kawayenta su martaba bukatun bai daya na kasashen yankin, su kauracewa bullo da rukunin fito na fito, da tashin hankali, da hargitsi a yankin Asiya da Fasifik. Har ila yau, Sin za ta himmatu wajen kare ikonta na mulkin kai da moriyar tsaronta, tare da kare halastattun hakkoki da moriyarta. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link