CMG Ya Yi Taron Tattaunawa Na Duniya Na “Sin A Lokacin Bazara” A Hadaddiyar Daular Larabawa

[ad_1]

Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, ya shirya tare da gudanar da taron tattaunawa na duniya bisa taken “Sin a lokacin bazara: Ci gaban Sin, dama ga duniya” a jiya Laraba 25 ga watan nan da muke, a birnin Abu Dhabi, fadar mulkin hadaddiyar daular Larabawa ko UAE. Kuma shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Kazalika, ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da masana, da wakilan kafafen yada labarai na Sin da UAE sama da 50 sun halarci taron.

A cikin ‘yan kwanakin nan, an gudanar da taron tattaunawa na duniya kan taken “Sin a lokacin bazara: Ci gaban Sin, dama ga duniya” a wasu kasashen nahiyar Turai da Latin Amurka, wadanda suka hada da Czech, da Moldova, da Jamus, da Italiya, da Bulgaria, da Finland, da Poland, da kuma Brazil da dai sauransu.

Mahalarta taron sun bayyana cewa, kasar Sin aminiya ce ta kasashen nahiyar Turai da Latin Amurka, inda suka yi hadin gwiwa wajen aiwatar da dangantakar cude-ni-in-cude-ka, da kuma fuskantar da kalubaloli tare, don haka ya kamata a zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu, domin cimma moriyar juna, da inganta dangantakar dake tsakaninsu, tare da habaka dunkulewar tattalin arziki, domin tallafawa al’ummomin duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *