Boko Haram ta file kan mata 2 a Borno

[ad_1]



Mayaƙan Boko Haram masu biyayya ga Ali Ngulde sun fille kan mata biyu a yankin Dutsen Mandara, Gwoza (Borno), bayan sun zarge su da yin shirka.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ƙungiyar kama matan ne da layu a lokacin bincike, inda a bidiyo da suka fitar, mayakan suka ce hakan shaida ce ta bin hanyar da suka kira haramtacciya.

An kai matan zuwa tsaunuka, aka aiwatar da hukunci a bainar jama’a domin tsoratar da mutane da kuma tilasta bin koyarwar ƙungiyar.

Rahotanni sun nuna cewa ɓangaren Ali Ngulde ya ƙara tsaurara matakan hukunci a ’yan watannin nan, inda ake kai hare-hare kan mutanen da ake zargi da sihiri, leƙen asiri, ko kuma yunkurin tserewa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *