Jakadan Sin a Najeriya Ya Wallafa Sharhi Don Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Diflomasiyya Tsakanin Sin Da Najeriya

[ad_1]

Jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai jiya Talata ya wallafa wani sharhi mai taken “Murnar cika shekaru 55 da kulla alakar diflomasiyya tsakanin Sin da Najeriya tare – Gina sabon babi wajen kirkiro makoma da gina al’umma ta bai-daya” a manyan jaridun Najeriya kamar su The Sun, The People’s Daily, da kuma The Guardian.

Sharhin ya nuna cewa, a ranar 10 ga watan Fabrairun 1971, Jamhuriyar Jama’ar Sin da Jamhuriyar Tarayyar Najeriya sun kulla alakar diflomasiyya a hukumance. A cikin rabin karni ko fiye da haka, Sin da Najeriya sun haye wahalhalu tare duba da sauyawar yanayin kasa da kasa, kana kasashen biyu ko da yaushe suna tafiya tare da fahimtar juna da fadada mu’ammala tsakaninsu, har sun kai ga kafa tushen huldarsu na mutunta juna da samun moriya tare cikin daidaito, wanda ya zama misali na hadin gwiwar kasashe masu tasowa.

Kazalika sharhin ya jaddada cewa, Sin da Najeriya wakilai ne na manyan kasashe masu tasowa dake da karfin tattalin arziki, wadanda ke da ra’ayi da bukatu iri daya a fagagen gudanar da harkokin kasashensu da gina tattalin arzikinsu. Dadin dadawa, suna kaiwa ga cimma matsaya daya da samun biyan bukatu iri daya a bangaren kare muradu na gama-gari na kasashe masu tasowa, da kuma gaggauta kyautata tsarin shugabancin duniya. Bangaren Sin yana matukar daraja dangantakar Sin da Najeriya, yana fatan fadada hadin gwiwa da bangaren Najeriya don tabbatar da muhimman yarjejeniyoyin shugabannin kasashen biyu da zamanantar da al’ummunsu cikin hadin gwiwa da gina hadakar kyakkyawar makomar al’ummunsu, duba da zarafi mai kyau na cika shekaru 55 da kafuwar huldar diflomasiyarsu da fara aiki da shekarar mu’ammalar al’adun Sin da Afirka ta 2026, ta yadda za su kawo fa’idodi ga jama’arsu da ba da gudunmawar a-zo-a-gani ta gina kyakkyawar makomar bil’adam ta bai- daya. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *