Da Gaske Ne Babu Tashar Samar Da Lantarki Ta Karfin Iska A Kasar Sin?


A gun taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na shekarar 2026 da aka gudanar kwanan nan ba da jimawa ba a birnin Davos na kasar Switzerland, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sake firgita duniya bisa kalamansa na wai “Kasar Sin ta kera dimbin injunan samar da lantarki ta karfin iska, amma ban taba ganin tashar samar da lantarki ta karfin iska ko daya a kasar Sin ba”.

Amma ko haka lamarin yake?

Masu karatu, idan kun samu damar zuwa kasar Sin, lallai kam akasin hakan za ku gani, duba da cewa, daga teku zuwa hamada, daga tuddai zuwa filaye, jerin injunan samar da lantarki ta karfin iska ne za ku gani a tsaye, wadanda suke juya karfin iska zuwa wutar lantarki tare da samar da su ga magidanta mabambanta. A lardin Gansu da ke arewa maso yammacin kasar, cibiyar samar da lantarki ta karfin iska ta Jiuquan na iya samar da lantarki da yawansa ya wuce KW miliyan 10, wanda har ma ake iya hango ta daga sararin samaniya sakamakon girmanta. Amma me ya hana shugaba Trump iya ganinta?

Ko kafofin yada labarai na kasashen yamma ma sun kasa hakuri da furucin shugaba Trump maras tushe, inda jaridar The Guardian ta kasar Burtaniya ta yi nuni da cewa, abin da ya furta ba gaskiya ba ne. A rahoton da jaridar ta wallafa, ta jaddada cewa, kasar Sin ita ce ta farko a duniya wajen iya samar da wutar lantarki ta karfin iska, har ma yawan lantarkin da take iya samarwa ta yin amfani da tashoshin samar da lantarki ta karfin iska da take ginawa ya ninka na sauran kasashen duniya baki daya sau biyu. Har ila yau, mujallar Time ta kasar Amurka ta ruwaito rahoton kwamitin kula da makamashin iska na duniya na GWEC yana cewa, a shekarar 2024, sabbin injunan samar da lantarki ta karfin iska da kasar Sin ta kafa sun dau kaso 70% na duniya baki daya, wadanda ke iya samar da lantarki da yawansa ya zarce GW 520, wato kusan rabi na duniya baki daya ke nan. Akwai kuma mai bibbiyar shafukan sada zumunta da ya bayyana cewa, “wani abokina ya dawo daga yawon shakatawa a kasar Sin, kuma ya gani da idonsa injunan samar da lantarki ta karfin iska da aka kafa kusan ko ina a kasar.”

Alal hakika, a cikin shekaru 10 da suka wuce, ayyukan samar da lantarki ta karfin iska sun bunkasa cikin sauri a kasar Sin, har ma kasar ta shiga sahun gaba a duniya. Ya zuwa karshen watan Nuwamban bara, yawan lantarki da kasar Sin ke iya samarwa ta karfin iska ya zarce KW miliyan 600, inda kasar ta kiyaye matsayinta na farko a duniya a fannin karfinta na wannan bangare tsawon shekaru 15 a jere. Sai dai adadin ba kawai ya bayyana saurin bunkasar kasar ta fannin yin amfani da karfin iska wajen samar da lantarki ba ne, har ma ya shaida irin sauye-sauyen da ke faruwa ga salon bunkasar kasar.

Hasali ma dai, baya ga kasancewarta kasa ta farko wajen samar da lantarki ta karfin iska a duniya, kasar Sin ta kuma kasance ta farko wajen samar da lantarki ta makamashin rana, kuma tana sahun gaba a duniya ta fannin samar da lantarki ta karfin ruwa. Hakan ya faru ne sakamakon irin fasahohin ci gaba da ma cikakken tsarin masana’antu masu alaka da sabbin makamashi da kasar ke da su a duniya, kuma ainihin abin da ya haifar da hakan shi ne manufar kasar Sin ta tabbatar da bunkasa ba tare da gurbata muhalli ba. Cimma burin kaiwa kololuwar fitar da hayakin Carbon zuwa shekarar 2030, da kuma kawar da illarsa zuwa shekarar 2060, ba kawai ya kasance alkawarin da kasar Sin ta dauka a gaban kasa da kasa ba ne, hatta ma wani abu ne da ita kanta take bukata wajen inganta ci gabanta.

A jawabin da ya gabatar a taron Davos, shugaba Trump ya ce, kullum kasar Sin na sayar da injunan samar da lantarki ta karfin iska ga “masu shirme”. Sai dai hakikanin abin da ya faru shi ne, kasar Sin na kokarin hadin gwiwa da sauran kasashe wajen tabbatar da bunkasa ba tare da gurbata muhalli ba, inda ta raba gajiyar nasarorin da ta cimma ta fannin rage fitar da hayakin Carbon ga kasa da kasa. A cikin ’yan shekarun baya, kasar Sin ta fitar da kayayyakinta masu alaka da samar da lantarki ta karfin iska da ta hasken rana da ma motocin lantarki zuwa kasashe da shiyyoyi sama da 200 a fadin duniya. Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, kayayyaki masu alaka da samar da lantarki ta karfin iska da ta hasken rana da kasar Sin ta fitar zuwa ketare sun taimaka ga rage fitar da hayakin Carbon kimanin tan biliyan 4.1 a kasashen. A sa’i daya kuma, sakamakon cikakken tsarin masana’antun samar da kayayyakin da ma fasahohinta masu ci gaba, kudin da kasa da kasa suka biya wajen samar da lantarki ta karfin iska da makamashin rana sun ragu da kaso 60% da 80% kowanensu. A nahiyar Afirka, kasar Sin ta aiwatar da hadin gwiwa da sama da rabin kasashen nahiyar ta fannin samar da sabbin makamashi, wanda hakan ya inganta harsashin kasashen wajen raya masana’antu da kuma zamanantar da kansu. To, maganar wayo ko shirme, tana kan wanda ya ga hakan ne.

Daga karshe, muna maraba da shugaba Trump da ya kawo ziyarar gani da ido tashoshin samar da lantarki ta karfin iska a kasar Sin, kuma tabbas injunan samar da lantarki ta karfin iska da aka kafa a sassa daban daban na kasar Sin za su ba shi amsa.



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *