Masana Sun Ba Da Shawarar Gyara Tsarin Filaye Domin Dakile Matsalar Tsaro
[ad_1]
Yusufu Bala Usman Institute ta gabatar da sakamakon bincike kan yadda ake tafiyar da kasa, kalubalen muhalli da kuma matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya.
An bayyana sakamakon binciken ne a wani taron manyan masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Laraba a Jamil Hotel da ke Azare, cikin Karamar Hukumar Katagum ta Jihar Bauchi.
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Zamfara
- Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Taron ya hada mahalarta daga sassa daban-daban na Jihar Bauchi, wadda ita ce daya daga cikin jihohin Arewa hudu da aka gudanar da wannan bincike. Sauran jihohin sun hada da Jihar Jigawa, Jihar Kaduna da Jihar Katsina.
Mahalarta taron sun hada da sarakunan gargajiya, shugabannin al’ummar Fulani, manoman Hausawa da kuma shugabannin addini, inda suka yi tattaunawa mai zurfi kan sakamakon binciken tare da nazarin hanyoyin magance manyan kalubalen da yankin ke fuskanta.
A yayin gabatar da binciken, Adam Higazi, wani kwararren mai bincike kan rikice-rikicen makiyaya da manoma a Nijeriya da Afirka ta Yamma, ya bayyana cewa kwace kasa da ‘yan siyasa da kamfanonin noma ke yi na daga cikin manyan dalilan da ke haddasa rasa kasa ga manoma da makiyaya a yankunan karkara.
“Raba kasa ga manyan ‘yan siyasa da kamfanoni na haifar da sare dazuka ba tare da tsari ba, mamaye wuraren kiwo da gandun daji, da kuma toshe hanyoyin dabbobi. Wadannan su ne manyan abubuwan da ke haifar da rikici da rashin zaman lafiya a yankin,” in ji shi.
Ya kuma lura cewa al’ummomin makiyaya, musamman Fulani, na ci gaba da rasa damar samun filayen kiwo, musamman a Jihar Bauchi, sakamakon kwace filaye, lalacewar muhalli da kuma yawaitar ayyukan dan adam.
“Hakan ya sa makiyaya da dama ke barin Jihar Bauchi zuwa wasu sassan Nijeriya da ma kasashen makwabta,” in ji Dakta Higazi.
Dakta Adam Higazi ya ba da shawarar haramta sare itatuwa ba bisa ka’ida ba, da farfado da gandun daji da wuraren kiwo kamar Rigar Itas a Karamar Hukumar Itas/Gadau da kuma Udubo Grazing Reserbe, tare da sake bude hanyoyin ruwa na dabbobi a fadin jihar.
Haka kuma, ya ba da shawarar kare hakkin mallakar kasa ga kananan manoma da makiyaya baki daya.
Mai binciken ya kuma yi kira da a gyara dokar amfani da filaye (Land Use Act) tare da kafa wata hukuma ta musamman da za ta kula da matsalolin makiyaya, noma da muhalli.
A nasa jawabin, Abdullahi Umar Eggi ya ce taron ya yi niyya ne don nazari mai zurfi kan batutuwan tafiyar da kasa, lalacewar muhalli da kuma karuwar matsalar tsaro.
Ya jaddada bukatar amfani da kwarewar masu ruwa da tsaki wajen tsara manufofi masu tasiri.
Da yake magana a madadin al’ummar Fulani, Sarkin Fulanin Katagum, Alhaji Muhammad Jauro Gari, ya bukaci gwamnati da ta dauki matakin gaggawa wajen magance kalubalen da makiyaya ke fuskanta.
Ya nuna damuwa kan ci gaba da raguwar wuraren kiwo da kuma tsanantar wahalhalu da makiyayan Fulani ke ciki.
Mahalarta taron sun yi irin wannan korafi, inda suka jaddada bukatar hadin gwiwar gwamnati wajen dakile sare dazuka, dawo da hanyoyin rayuwa da kuma karfafa zaman lafiya da tsaro a Arewacin Nijeriya.
An kammala taron da kira na bai daya kan ci gaba da tattaunawa da daukar matakan manufofi masu karfi domin magance tushen rikice-rikicen kasa da kalubalen muhalli a yankin.
Hukumar kasa Birtaniya ta (UK Foreign, Commonwealth and Debelopment Office (FCDO) ta dauki nauyin gudanar da binciken ta hannun Shirin samar da zaman lafiya ta (Strengthening Peace and Resilience in Nigeria (SPRiNG).
[ad_2]
Source link