Bayan Shekaru 7, DSS Ta Sake Buɗe Binciken Ɓacewar Dadiyata

[ad_1]

Hukumar Tsaro ta DSS, ta sake buɗe bincike kan sacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, lamarin da ya faru a 2019. Rahotanni sun ce hukumar na shirin gayyatar wasu da ake zargi, ciki har da ‘ya’yan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, domin yi musu tambayoyi.

An sace Dadiyata, malami a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma da ke Jihar Katsina, a gidansa da ke Barnawa, Kaduna, ranar 2 ga Agustan 2019. Zuwa yanzu, kusan shekaru bakwai kenan ba a san inda yake ba.

  • DSS Ta Kama El-Rufai Bayan EFCC Ta Bayar Da Belinsa
  • Kiyaye Ci Gaba Mai Dorewa A Huldar Sin Da Amurka Ya Dace Da Moriyar Sasssan Biyu

A wata hira da ta yi da tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Reno Omokri, matar Dadiyata, Kadijah, ta bayyana fargaba kan ɓacewar mijinta, tana mai roƙon ‘yan Nijeriya su taimaka wajen gano gaskiyar lamarin. Ta kuma tuna wani saƙo da aka wallafa a kafafen sada zumunta a 2019 da ta ce ya ƙunshi “ƙarya mai haɗari”.

Da yake mayar da martani, El-Rufai ya musanta sanin Dadiyata ko hannu a lamarin, yana cewa batunsa ya fi shafar siyasar Kano. Shi ma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ta bakin mai magana da yawunsa Muhammad Garba, ya wanke kansa daga zarge-zargen, yana mai kiran su marasa tushe.

Wata majiya ta tsaro ta ce DSS ta kwace fasfon El-Rufai a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a matsayin ɓangare na binciken da ake ci gaba da yi kan batun Dadiyata da sauran mutanen da suka ɓace.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *