Makomar Nijeriya Na Hannun FIFA – Shehu Dikko
[ad_1]
Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa, (NSC), Shehu Dikko, ya ce makomar Nijeriya a gasar Kofin Duniya ta 2026 yanzu na hannun FIFA, bayan ƙarar da NFF ta shigar kan zargin cewa Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ta saka ’yan wasan da ba su cancanta ba a wasan neman gurbin shiga gasar.
Da yake ganawa da manema labarai bayan wata ganawa da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a Fadar Shugaban Ƙasa, Dikko ya ce a ɓangaren gasa an riga an rufe shafin, amma batun shari’a na nan a gaban hukumomin da suka dace a FIFA. Ya ce hukuncin ƙarshe zai fito ne daga hukumomin cikin gida na FIFA masu zaman kansu.
- Me Ya Sa Karin Kasashen Duniya Ke Yin Na’am Da Bikin Bazara?
- Shugabannin Duniya Sun Taya Sin Murnar Sabuwar Shekarar Doki
Dikko ya yi fatan cewa har yanzu akwai yiwuwar a dawo da Super Eagles cikin jerin ƙasashen da za su fafata a wasan neman tikitin ƙarshe na nahiyoyin da za a buga a watan Maris, idan har FIFA ta yanke hukunci a madadin Nijeriya.
Yanzu dai idon duniya na kan hukuncin da FIFA za ta yanke, wanda zai tantance ko Nijeriya za ta samu wata sabuwar dama ta komawa fafatawa a gasar Kofin Duniya ta 2026.
[ad_2]
Source link