Ba ma tsoron a ƙirƙiro ’yan sandan jihohi — Disu

[ad_1]



Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya ce a shirye yake ya yi aiki domin ganin an samar da rundunar ’yan sandan jihohi a faɗin ƙasar nan.

Disu, ya kuma tabbatar wa jami’an ’yan sanda cewa samar da ’yan sandan jihohi ba zai zame musu barazana ba.

Ya bayyana haka ne yayin da yake magana da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da shi a ranar Laraba.

Disu ya kuma yi alƙawarin cewa ’yan sanda za su bi hanyoyin ƙwarewa wajen magance zanga-zangar da ake yi a wasu sassan ƙasar dangane da halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.

Ya ce rundunar ’yan sandan Najeriya a shirye take ta haɗa kai da ’yan sandan jihohi idan aka kafa su.

“’Yan sandan jihohi abu ne da zai iya tabbata, kuma ’yan sanda za su taka rawarsu domin ganin ya yi nasara. Ba ma jin tsoro. Ba za a ƙwace mana aiki ba. Maganar haɗin gwiwa ce kawai,” in ji shi.

Disu ya bayyana cewa ’yan sanda na sa ido kan ƙungiyoyi daban-daban da ke cikin ƙasar nan.

Ya ce abubuwan da ke faruwa a wasu sassan duniya na iya shafar wasu mutane a Najeriya, musamman ƙungiyoyin da ke nuna goyon baya ga wasu yankuna na duniya.

Ya ce ’yan sanda na ɗaukar matakai domin hana aukuwar tashin hankali.

A cewarsa, an tura jami’ai sintiri a wurare daban-daban, kuma suna tattaunawa da wasu ƙungiyoyi domin tabbatar da cewa ba wanda zai ɗauki doka a hannunsa.

Game da yadda zai tafiyar da aikinsa, Disu ya ce yana son jami’an ’yan sanda su fahimci cewa suna aiki ne domin al’ummar Najeriya.

“Muna aiki ne domin al’ummar Tarayyar Najeriya, kuma su ne shugabanninmu,” in ji shi.

Disu ya kuma yi magana kan kwamitin da ya kafa da safiyar ranar Laraba domin duba batun ’yan sandan jihohi.

Ya ce dole ne ’yan sanda su tattauna batun, domin su ne mafi kusa da abin da zai shafa.

Sufeto-Janar ɗin ya ce aikin ’yan sanda aiki ne mai wahala da hatsari.

Ya tuna lokacin da yake Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ’yan sanda 140 sun rasa rayukansu cikin shekara guda.

A cewarsa, jami’ai da dama na yin aiki na dogon lokaci, wasu kan kwana a bakin aiki, kuma da yawa ba sa samun damar komawa wajen iyalansu saboda yanayin aiki.

Saboda haka ya ce kula da jin daɗin jami’an rundunar na da matuƙar muhimmanci.

Ya ƙara da cewa ya yi sa’ar yim aiki tare da Shugaba Tinubu, wanda ya ƙudiri aniyar tallafa wa rundunar da abin da suke buƙata.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *